Ebola Ta Sake Bulla A Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Ebola Ta Sake Bulla A Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Published

on


Mahukunta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce annobar Ebola ta bulla a wani yanki na daban da ke gabashin kasar, bayan da aka yi shelar cewa an shawo kan cutar bayan da ta kashe mutum 125 a cikin watannin da suka gabata.

Ministan lafiyar kasar Oly Ilunga, ya ce annobar ta bulla ne a wani wuri da ke tsakiyar Beni, a lardin Kibu ta Arewa kusa da iyakar kasar da Uganda.

Ministan ya ce an samu bullar cutar a wannan yanki ne sakamakon yadda jama’a ke ci gaba da bijire wa matakan mahukunta ke dauka domin hana yaduwar cutar ta Ebola.

Advertisement
Click to comment

labarai