‘Yan Sanda Sun Nuna Wadanda Ake Zargi Da Kashe Jami’ansu A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Nuna Wadanda Ake Zargi Da Kashe Jami’ansu A Kaduna

Published

on


A jiya ne rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna ta nu na wa manema labarai mutanan da ake zargi da kashe Jami’anta hudu, a unguwar Jankasa, da ke gundumar Rigasa, ta Jihar Kaduna.

Rundunar kuma ta nu na wadanda ake zargi da kashe wasu ‘yan sandan biyu a kan hanyar Birnin Gwari.

Da yake nu na wadanda ake zargin, mukaddashin Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Ahmed Magaji Kontagora, cewa ya yi, a ranar 16/08/2018, rundunar musamman ta babban sufeton ‘yan sanda na kasa bisa hadin gwiwa da rundunar, Operation Yaki, sun kai farmaki wata maboyar ‘yan fashi da makami da kuma masu satan mutane da ke kan hanyar kauyan Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi.

Kontagora ya ce, bayan musayar wuta da batagarin, mun ji wa biyu daga cikinsu munanan raunuka, an kuma tabbatar da mutuwar su ne bayan da aka kawo su asibitin Barau Dikko, Kaduna.

A cewar shi, “Bayan farmakin kwantan bauna da suka aiwatar a kan Jami’an namu a kauyan Jankasa, da ke gundumar Rigasa, ta karamar hukumar Igabi, a ranar 11 ga watan Agusta 2018, sai muka tsananta farautar wadanda suka aikata laifin da ma sauran masu aikata ayyukan ta’addanci a yankin domin mu kama su mu fuskantar da su ga shari’a.

“A wannan samamen, ina farin cikin sanar da ku cewa, mun kwato bindigar AK47 da harsasai masu rai guda biyar daga hannun ‘yan ta’addan, wadanda su ne suke addaban al’umman Birnin Gwari da sassan ta, su ne kuma suka kashe, Insifikta Felid Yohanna, a dajin Walawa da kuma wasu Jami’an ‘yan sandan hudu da aka kashe kwanan nan a harin kwantan bauna a kauyan Jankasa.

“Hakanan kuma, rundunar tamu masu yaki da ‘yan fashi da makami ta FSARS, da kuma rundunarmu ta SIB, sun sami nasarar kama mutane bakwai da ake tuhuma da satar mutane, da kuma mutane takwas da ake tuhuma da aikata fashi da makami gami da wasu mutane hudu wadanda suka shahara da ayyukan zamba. Da wasu mutane uku masu fasa shaguna suna sata, mun kuma kwato bindigogin AK47 guda uku, da kurtun albarusai guda uku, tare da harsasai masu rai guda 20, motoci guda biyu, daya kirar, Golf Wagon mai dauke da lamba kamar haka, ES904FST, dayar kuma, Toyota Corolla mai lamba, RBC04MK dukkan su masu launin toka.”

Mukaddashin Kwamishinan yace, da zaran sun kammala na su binciken za su gabatar da wadanda ake tuhuman a gaban kotu.

Advertisement
Click to comment

labarai