Wadanda Ake Zargi Da Kashe ‘Yan sanda Hudu Sun Shiga Hannu A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Wadanda Ake Zargi Da Kashe ‘Yan sanda Hudu Sun Shiga Hannu A Kaduna

Published

on


A ranar Alhamis ce Rindinar ‘ yan sanda ta jihar Kaduana ta  baje kolin wasu mutane su hudu da take zarginsu da kashe mata jami’anta guda hudu.

‘yansandan hudu da aka a kashe suna gudanar da aikinsu ne kai tsaye daga ofishin shugaban ‘yan sanda na kasa kuma an kashe su ne a wani artabau da aka yi a yankin Jankasa da ke cikin gundumar  Rigasa a cikin jihar Kaduna a lokacin da suka kai samame..

Haka kuma, rindinar ta kuma baje kolin wasu da ta ke zargi da hallaka mata ‘yan sanda biyu a kan hanyar Birnin Gwari  da ke cikin jihar ta Kaduna.

A cewar kwamishina ‘yan sanda mai rikon kwarya na jihar Ahmed Magaji Kontagora,  a ranar  16/08/2018 jami’an na musamman daga ofishin shugaban ‘yan sanda na kasa tare da  jami’an Operation Yaki, sun kai farmaki a kan ‘yan fashi da makami da kuma masu sace mutane a mafakarsu da ke kauyen Sabon Birni a cikin karamar hukumar Igabi.

Kontagora ya kara da cewar, bayan bayan artabun da ‘yan sandan sun jiwa ‘yan bindiga dadi biyu raunuka inda daga bayan an kai su asibitin Barau Dikko  da ke cikin jihar aka tabbatar da mutuwar su.

Ya kara da cewar, bayan artabun na kauyen Jankasa, yansandan su kuma bazama wajen cafko sauran wadanda suka gudu don a hukunta su kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ci gaba da cewar, ‘yan sandan sun kuma kwace bindiga kirar AK47 daya da kwabsar albarusai guda biyar  a inda akayi artabun.

Kontagora ya bayyaba cewar, a bisa binciken daaka guidanar, an gano cewar ‘ yan ta’addar suna daya daga cikin gungun makasan da suka jima suna addabar yankin Birnin Gwari  kuma sune suka kashe wani Insfekta mai suna Felid Yohanna a dajin Walawa dake  kauyen Jankasa.

Ya kuma sanar da cewar, sun cafke masu sace mutane da ake zargi su bakwai da ‘ yan fashi takwas da masu damfara su bakwai  da masu fasa shaguna su uku da kuma kwace bingogi kirar AK47  uku da kwabsar albarusai ashirin da motoci biyu  kirar Golf Wagon mai lamba ES904FST da  Toyota Corolla mai lamba  RBC04MK.

A karshe Kontagora ya ce in rindinar ta kammala bincike , zata  gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai