Sarkin Zazzau Ya Yaba Wa Gwamnatoci Kan Tsaro - Sarkin Filinin Zazzau — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sarkin Zazzau Ya Yaba Wa Gwamnatoci Kan Tsaro – Sarkin Filinin Zazzau

Published

on


Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya yaba wa gwamnatin tarayya da kuma gwanatocin jihohi na yadda suka jajirce na bin hanyoyin da suka kamata domin kara samar da ingantaccen tsaron lafiyar al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Sakataren masarautar Zazzau kuma Hakimin Damau, Alhaji Barau Musa Aliyu, ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da jawabin mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, a lokacin gaisuwar Faada, wada aka saba yi a duk ranar Hawan daushe, da safe a gaban mai martaba Sarkin Zazzau.

Wannan kokari da mai martaba Sarkin Zazzau ya ke yi, a cewar Sakataren masarautar Zazzau, muhimmin aiki ne da ya haifar da ‘ya’ya ma su ido a batun tsaro da a shekarun baya matsalar na gab da zama gagara – badau ga gwamnati.

Kan wadannan nasarori da gwamnatin tarayya ta samu kan matsalar tsaro, kamar yadda Sarkin Damau ya ce, mai martaba Sarkin Zazzau ya gudanar da taron hadin gwiwa da jami’an tsaron da suke masarautar Zazzau, inda aka tattauna abubuwa da yawan gaske, na yadda za a kawar da ta’addanci da ke faruwa a cikin al’umma, da suka shafi yin garkuwa da mutane da ma su satar shanu da matsalar fashi da makami da dai sauran matsaloli ma su yawan gaske.

A duk karshen taron da mai martaba Sarkin Zazzau ke jagoranta a fadar Zazzau, a karshen taron, mai martaba Sarki kan mika wa gwamnati rahotannin taron da aka yi, da yada za a warware matsalolin da aka gano, domin a warware matsalolin a cikin dan kankanin lokaci, daga bangaren gwamnati.

Alhaji Barau Musa Aliyu, ya kuma ce, mai martaba Sarkin Zazzau, ya umurci hakimai da kuma sauran shugabannin al’umma da su rika gudanar da irin wannan taron a gundumominsu, domin a sami damar murkushe duk wasu ‘yan baya ga dangi da suke labewa a cikin al’umma, suna aikata ta’asa, kamar fashi da makami da garkuwa da mutane da dai sauran muggan ayyuka, da suke durkusar da al’umma.

A dai jawabin mai martaba Sarkin Zazzau da Sarkin filanin Zazzau ya karanta, ya jawo hankalin al’umma da`suka mallaki gonaki, kuma suna sayarwa ga wasu gurbatattun mutane da ba a san inda suka fito ba,’ wannan babbar matsala ce mai zaman kanta da take neman gyara, domi tabbatar da tsaro, kamar yadda gwamnatin tarayya ta sa wa gaba’’.

Game da sabbin gine-gine da ake yi a sassa daban-daban na masarautar Zazzau, mai martaba Sarki ya yi kira ga Hakimansa da dakatai da ardo-ardo da ma ma su Unguwanni , da su kara sa hajar mujiya, na ganin sun gano dalilan da suka sa bata-gari suka mayar da wadannan gine-gine matsuninsu, kuma su gabatar da binciken da suka a boye,tare da shaida wa jami’an tsaro a kan lokaci, Domin bunkasa ilimi a masarautar Zazzau kuma, sai Sakatren masarutar Zazzau ya yi kira ga tsofaffin malaman makaranta da kuma kungiyoyin da aka kafa su domin ci gabamn ilimi, da su rubanya tallafin koyar da yaran da suke yi, domin yaran su sami saukin rubuta ko wace irin jarabawa, ta gaba da sakandare.

Kan dai batun ilimi, Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya umurci Daukacin hakiman masarautarsa da kuma ardo – ardo, su rika ziyarar makarantun da suke gundumominsu, domin sanin abubuwan da suke gudana a makarantun, in an ga wata matsala, mai martaba Sarkin Zazzau ya ce, sai su  gabatar da matsalolin da suka gano, domin daukar matakan da suka dace, da zai inganta ilimi ako wane mataki ko kuma matakai.

A fagen kiwon lafiya kuma, mai martaba Sarki ya umurci iyayen yara da su rika kai yaransu cibiyoyin yin ko wane irin rigakafi, na cutuutukan da suke yi wa yara kamun kazar kuku, wannan zai taimaka yaran su sami koshin lafiya a tsawon rayuwarsu.

Wannan taron gaisuwar Fada da aka saba gabatar wa a masarautar Zazzau,ta sami halartar daukacin Hakiman masarautar Zazzau, da manyan

malaman addinin musulunci da kuma wasu fastoci da suka fito daga Wusasa.

Advertisement
Click to comment

labarai