Sanata Shehu Sani Ya Kai Wa Buhari Ziyara A Daura — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sanata Shehu Sani Ya Kai Wa Buhari Ziyara A Daura

Published

on


A ranar Alhamis ne Sanata Shehu Sani, ya kai wa Shugaba Buhari gaisuwan Sallah a garin Daura, inda kuma ya yi ma shi godiya kan tsalma bakin da ya yi a kan rikicin da ya addabi Jam’iyyar APC a Jihar ta Kaduna.

Da yake magana da manema labarai bayan fitowar sa daga ganawar sirrin da Shugaban kasan, Sanata Shehu Sani, yace sun tattauna ne a kan yadda za a karfafa Jam’iyyar ta APC ta hanyar warware dukkanin sabanin da yake a tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar.

A cewar sa, ya kuma yi amfani da wannan daman wajen tabbatar wa da Shugaban kasan da goyon bayan al’umman mazaban sa na sake zaban sa a shekarar 2019.

“Sannan na kuma zo ne domin na tabbatar masa da goyon bayana kacokan kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kuma goyon baya na, na ganin ya sake komawa bisa kujerar na shi a karo na biyu.

“Wadannan su ne manyan abubuwan da muka tattauna, sai kuma wasu abubuwan da za su karfafa Jam’iyyar namu, kamar bukatar kawo karshen rigingimun cikin Jam’iyyar da yadda za a hada karfi wajen ganin samun nasarar gwamnatin da kuma Jam’iyyar.”

Sanata Sani yace, shawarar da ya yanke na ci gaba da zama a cikin Jam’iyyar ta APC, ba wai ya yi hakan ne domin an warware dukkanin rikicin da ke a tsakanin sa da shugabannin Jam’iyyar ne a Jihar ta Kaduna ba, ya yi hakan ne a bisa sanya bakin da Shugaba Buhari da kuma shugabannin Jam’iyyar suka yi masa.

“Ba wani mutum da ba shi da wata damuwa, amma in ana maganan kasa akan ajiye son kai ne a gefe.

A kan ko an yi ma shi alkawarin tikitin sake tsayawa takarar Sanatan ne a zaben 2019, Sani yace, shi kansa ba son tikitin kai tsaye yake yi ba, sai dai Jam’iyyar ta yi alkawarin sakankama wadanda suka yi mata biyayya.

Sai dai yace, duk da an yi wa ‘ya’yan Jam’iyyar alkawarinsakamakon biyayyan da suka yi, amma dai tilas ne a bi ta hanyar da doka ta tanada.

“Ba maganan tikitin kai tsaye ne a gabanmu ba, babban fatan mu itace ganin an gudanar da zaben cikin gaskiya kuma lami lafiya, sannan kuma ya zama tilas kowannen mu ya san cewa, makomar fa wannan kasan tana hannun mu ne.

“Akwai bukatar mu yi watsi da duk wani sabanin kabilanci ko na Addini domin ci gaban kasarmu, sannan kuma kasantuwan Shugaban kasa da kuma Shugaban Jam’iyyarmu sun sanya baki, ina da tabbacin dukkanin rikicinmu na cikin gida duk za su zo karshe.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai