Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Yi Barna A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Yi Barna A Kaduna

Published

on


Ruwan sama da akayi a ranar Alhamis data gabata a jihar Kaduna wanda kuma shafe awowi ana yinsa, a wasu sassan jihar Kaduna ya yi albaliya a wasu hanyoyin dake cikin jihar.

Ruwan saman ya fara zuna tunda wajen misalign karfe daya na dare haka, inda hakan ya janyo matafiya na kasa dana kan ababen hawa dole suka samu wajen fakewa.

Har ila yau,  cike wasu gidajen tare da rusa wasu katangun gidaje da kuma ciki magudana ruwa.

Hukumar  kare muhallai ta jihar Kaduna KEPA, tun ta yi gargadi akan cewar masu gidaje su su sanya ido su nkuma ankare akan yuwar ambaliyar ruwa.

Har ila yau, hukumar bayar agajin gaggawa ta jihar SEMA itama ta gargadi mutanen akan yuwawa samun ambaliyar rowan sama da kuma ballewar rafukka akan cewar duk gidajen dake a banin ruwa su tashi don gudun barkewar amabliyar ruwa.

Bugu da kari, hukumar auna yanayi NIMET a kwanan baya ta yi kirdadon cewar jihar Kaduna zata fuskanci ambaliyar rowan sama musamman a wuraen da suke kusa da rafukka a jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai