Mutum Hudu Sun Fada Komar ‘Yansanda A Bisa Zargin Sayar Da Jarirai — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Mutum Hudu Sun Fada Komar ‘Yansanda A Bisa Zargin Sayar Da Jarirai

Published

on


A ranar Juma’a ce Rindinar ‘yansanda ta jihar Enugu ta sanar da cewar, ta cafke mutane hudu da take zargi da shirin sayar da jarirai a cikin garin na Enugu.

Kakakin rindinar SP Ebere Amaraizu ne ya sanar da hakan a cikin sanarwar day a fitar a jihar, inda yace wadanda ake zargin sun aikata hakan ne a ranar 21 ga watan Agustan wannnan shekarar.

Acewar sa, an damko su ne bayan da rindinar ta samu bayanan sirri akan yunkurin nasu, inda rindinar ta umarci jami’anta dake ofishin ‘yansanda na gundumar Awkunanaw  suka kamo su.

Ya kara da cewar, wadanda ake zargin sun kware wajen sayar da jarirai da kuma safarar mutane.

Ya zayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka,  Amarachi Igwe, Chekwube Ofornwa, Gidi Mohammed wadanda uku sun fito ne daga yankin sabuwar  dake Awkunanaw saikuma sai Ndubuisi Eze fito daga yankin Abakpa dake cikin jihar.

Kakakin ya kara da cewar, dubunsu ta cika ne a lokacin da suke yinkurin sayar da jariri dan wata biyu, inda yace wadanda ake zargin suna baiwa ‘yansanda hadin kai a bisa binciken da akeyi akansu .

Advertisement
Click to comment

labarai