Kowace Sallah Muna Wadatar Da Legos Da Kayan Miya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kowace Sallah Muna Wadatar Da Legos Da Kayan Miya

Published

on


Kayan miyan da suka jibanci tattasai da tarugu da tumatur da sauran abubuwan da ake hada wa domin miya, musamman wadansu abubuwa ne da suke da mahimmanci a wajen Abincin da dan’adam.

Alhaji Aminu Musa Baban Iyabo shi ne sakataren shugaban kungiyar ‘yan tattasai karkashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Dauda Tarai da ke Babbar kasuwar sayar da kayan gwari da ke Mile 12 ta jihar Legos.

Sakataren ya ce a kowace Sallah ta Musulmi ko ta Kiristoci a wannan kasuwa mai Al-barka ta kayan abinci suna wadatar da Al-umar jihar Legas da abinci Alhaji Aminu Musa ya ci gaba da cewa wannan kasuwa ta Mile 12 Babbar Kasuwace da Al-umar Jahar Legas ke amfana da ita kai dama sauran kasashen ketare da ke makwabtaka da Jahar Legos ke shigo wa domin sayan abin sa wa a bakin salati ya kara da cewa a wannan sallarma wannan Kasuwa ta Mile 12 wadda Allah ya Albar kace ta da kayan abinci nau’i daban-daban da Al’ummar Nijeriya da sauran wadansu kasashen duniya da ke makwabtaka da ita ke yin sana’a kuma suke samun abinci suna ci a kowace rana da izinin Allah za su tabbatar da kowa ya sayi abincin sallah a cikin sauki.

Sannan ya yi kira ga Gwamnatin ta Rayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka wajen gyaran hanyoyin da motoci ke amfani dasu wajen kawo wadannan kayan abinci daga Arewacin Nijeriya zuwa jihar Legas bisa ga kokarinsa na gudanar da irin wannan ayyuka a Nijeriya kowane lokaci.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai