Dalilin Da Ya Sa Na Yi Tattakin Mita 800 A Daura –Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dalilin Da Ya Sa Na Yi Tattakin Mita 800 A Daura –Buhari

Published

on


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya yi tattaki na tsawon mita dari tawas a garin Daura ranar Sallah.

Buhari  ya ce ba ya yi tafiyar ba ne domin ya nuna wa jama’a cewa yana da lafiya ko wata manufa ta siyasa, ya kuwa bayyana hakan ne lokacin da suke zaman tattauna wa da shugabannin kananan hukumomi guda biyar da ke yankin na Daura

Wakilinmu ya jiwo mana cewa, wasu na ta yamadidin cewa Buharin ya yi wannan tafiyar ce domin ya nuna wa ‘yan Nijeriya cewa, yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya ci gaba da jagorancin kasar nan.

Mai ba shugaban kasar shawara na musamman a kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu,ya ce, Buhari ya ce: ‘

“ Na zo giada ne jama’a da dama sun fito su gan ni, kuma motar da nake ciki gilasjinta mai duhu ne saboda haka na ga ya dace in fito in tattaka a kafa domin duk wanda ke sun ganina ya gan ni.

‘‘Saboda haka maganar tsaya wa takarata tuni na bayyana wa jama’a a, saboda haka wannan tattakin da na yi, ba na yi ba ne domin cim ma  burina na siyasa ba.”

Lokacin ganawar Buharin da ‘yan majalisar sarki ya yi musu albishir da cewa, yanzu haka ya bayar da umarni ga ma’aikatar gona da  Babban Bankin kasa da su samar da basussuka ga kananan manoma, domin a tallafa musu yadda za su bunkasa sana’ar ta su ta noman.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai