An Bai wa Mataimakin Gwamna Sarautan Kafisu A Nasarawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Bai wa Mataimakin Gwamna Sarautan Kafisu A Nasarawa

Published

on


Masarautar Karshin da ke yankin raya kasa na Karshi a Karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa, ta nada Mataimakin Gwamnan Jihar Mista Silas Ali Agara a matsayin Sarautar Kafisu na Karshin.

Nadin Sarautar da ya gudana a ranar Laraba  a fadar  Sarkin Karshin, Alhaji Ahmad Abdullahi Hasan, wanda ake wa lakabi da, ‘Yankanajeh,’ da ke garin karshin. Shi ya tabbatar da wannan nadin da kansa a lokacin da Mataimakin Gwamna, Honorabul Silas Ali Agara, ya je gaisuwar Sallah a fadar na sa da ke Karamar Hukumar Karu, a ranar Laraban kashegarin Sallah.

Masarautar ta ce, ta duba cancantarsa a matsayinsa na mutumin da ke da daraja na biyu a Jihar Nasarawa, amma bai dauki kansa a bakin komai ba, yana biyayya ga mutane yadda ya kamata.
Kuma yana tafiyar da aikinsa bisa turbar gaskiya da rikon amana tsakaninsa da maigidansa da ma dukkanin al’umman Jihar.

Ta ce, saboda haka, wannan shi ne sakayyar goron  Sallar da za mu ba ka, kamar yadda muka tabbatar ba ka da nauyin kafa muka nada maka wannan Sarauta na cancanta mai suna, ‘Kafisu.’

Da yake mayar da jawabi ta bakin Jami’in yada labaransa, Godspower Ede, Mataimakin Gwamnan, Honorabul Silas Ali Agara, ya yi dubun godiya da samun wannan mukamin da bai taba yin mafarkin zai same shi a irin wannan lokacin ba.
Mataimakin Gwamna ya ce, “abin da ba mu yi tsammani ba, sai ga shi mun same shi saboda mun zo gaisuwar Sallah ne kamar yadda muka sa ba duk Shekara, sai ga shi Ubanmu, Mai Martaba Sarkin Karshin ya nada mani wannan Sarautar,  wacce  kuma zan yi alfahari da ita komai daren dadewa ba zan manta da wannan ranar ba.”

Ya kuma mika dubun godiya ga Masarautar Karshin da al’umman yankin raya kasa ta Karshin da al’umman Jihar Nasarawa bakidaya.

Advertisement
Click to comment

labarai