Aiyukan Gwamnatin Tarayya 69 Ke Ci Gaba Da Gudana A Kudu Maso Gabas--- Lai Muhammed — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Aiyukan Gwamnatin Tarayya 69 Ke Ci Gaba Da Gudana A Kudu Maso Gabas— Lai Muhammed

Published

on


Ministan yada labarai, al’adu da yawon bude ido, Alhaji Lai Muhammed ya maida martani ga bayanin da wasu gwamnonin shiyyar Kudu Maso Gabas suka yi; da ke cewa gwamnatin tarayya ta gaza wajen gudanar da ayyukan raya birane a shiyyar wanda suka ce gwamnatin mai ci ta maida su saniyar ware ta fuskacin samar da aiyukan more rayuwa.

Ministan wanda ke shaida hakan a Alhamis din nan a garin Illorin ta jihar Kwara a yayin da ke jawabi kan ayyukan Buhari da na Osinbajo 2019, inda ya shaida cewar a yanzu haka ayyukan da gwamnatin tarayya take gudanarwa sun kai  69 a wannan shiyyar ta Kudu maso gabashin Nijeriya.

Ministan ya shaida cewar a dukkanin shiyyoyin da Nijeriya take da su, gwamnatinsu tana gayar adalci wajen rabon aikace-aikace, don haka ne ma ya shaida cewar a shiyyar Kudu Maso gabas ayyukan suna gudanuwa kamar yadda gwamnatin tarayya take bayarwa a wasu rassan kasar nan.

Ya kara da cewa, daga cikin aikace-aikacen da gwamnatin tarayya take yi a titinin hanyoyin, akwai wadanda gwamnatin baya ta bayar da su amma a sakamakon gaza fitar da kudaden aiyukan hakan ya sanya aiyukan ba su keta karshen da ake son su kai ba.Lai Muhammed ya dai jero wasu daga cikin ayyukan da a yanzu haka gwamnatinsu ke kan gudanarwa a wannan yankin, inda ya yi amfani da wannan damar wajen shaida cewar shiyyar Kudu maso gabas na gayar samun kulawa daga wannan gwamnatin, inda yake bayanin cewar ayyukan da ake aiwatar na hanya ba a samu irinsu a gwamnatin baya ba.

“Abin mamaki ne wani ya fito ya ce wai babu wasu ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a shiyyar Kudu Maso Gabashin kasar nan, alhali ga tulin aiyuka birjik kuma a baiyane, ga jerin tagwayen hanyoyin da ake kan shimfidawa ga titian da manyan hanyoyi a wannan yankin amma duk da haka wani ya ce ba a komai,” Kamar yadda ya shaida

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai