Matakin Da Buhari Ya Dauka Kan Mayar Da Tsohon Shugaban DSS Kujerarsa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Matakin Da Buhari Ya Dauka Kan Mayar Da Tsohon Shugaban DSS Kujerarsa

Published

on


An bayar da rahoton cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya kore yiwuwar sake mayar da tsohon babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, Lawal Daura, wanda mukaddashin  Shugaban kasa a wancan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sauke a kan kujerarsa. Jaridar turanci ta, ‘The Nation,’ ta kawo rahoton duk da matsin lamba daga wasu na kusa da shugaban kasan suka yi ta yi masa, amma Shugaban kasan ya kore yiwuwar hakan. Wata majiya ta tabbatar da cewa, Shugaban kasan ba shi da wata manufa ta dawowa da Daura din. majiyar ta ce, maganan ma da ake yi a yanzun ita ce ta tabbatar ma da mai rikon kujerar, Mathew Seiyafa, shugabancin hukumar a matakin babban daraktan hukumar.

Majiyar ta ce, “Masu kokarin ganin an mayar da Daura din bisa kujerar ba su yi nasaran hakan ba, domin tuni Shugaban kasa ya rufe yiwuwar dawowa da shi din. Sam Shugaban kasa ba shi da wata manufa ta dawowa da shi ko ta wace hanya. Shugaban kasan ya yi imani da cewa wannan gwamnatin ta su ce shi da Osinbajo, ba yadda Osinbajo zai gitta kara shi kuma ya gusar da shi. “Abin da ya faru shi ne, wasu Ministoci ne da kuma wasu kalilan na kusa da Shugaban kasan hadi da wasu manyan mutane da su ma suke kusa da Shugaban kasan, suka sulale zuwa London, suka iske Shugaban kasan suna masa magiyan ya canza hukuncin da mataimakin na shi ya zartar na korar Daura din, ya kuma dawo da shi a kan kujerar.

“Su ba su san cewa, Shugaban kasan da mataimakin na shi sun rigaya sun tattauna a kan korar Lawal Dauran ba, da ma wasu shugabannin jami’an tsaro, akalla makwanni biyu kafin Shugaban kasan ya wuce zuwa hutun na shi a London. Shugabannin biyu sun yi matsaya a kan wajibcin yin wasu canje-canje. Wanda hakan ya sanya duk abin da Osinbajo din ya yi, ya yi ne a kan abin da suka rigaya suka tsara da Shugaban na shi.”

An ce wani tsohon Shugaban kasar nan da kuma wani Minista ne suka yi magana da Shugaba Buhari a sa’ilin da yake hutun na shi a London, inda suka shawarce shi da kar ya sake mayar da Lawal Daura din. “Wani tsohon Shugaban kasa tare da wani Minista cikin Ministocin da ke kusa da Buhari din ne suka shawarce shi da ya yi watsi da duk wasu masu kiran sa da ya mayar da Daura din, domin tabbatar da bin tsarin Dimokuradiyyan da gwamnatin na shi ta yi na korar Lawal Dauran bayan ya tura jami’an sa sun mamaye  Majalisun kasa ba tare da izinin yin hakan ba.

“Tsohon Shugaban kasan ya ja kunnin Shugaba Buhari, kan irin martanin da kasashen duniya za su dauka matukar ya dawo da Lawal Daura din a bisa wannan kujerar,” in ji majiyar tamu. Wata majiyar kuma ta tabbatar mana da cewa, Shugaba Buhari ya goyi bayan matakin korar Lawal Dauran da Osinbajo ya yi. majiyar ta ce, “Tabbas da gaske ne, Mukaddashin Shugaban kasan, Osinbajo, ya kori Lawal Daura ne daga mukamin na shi tun kafin ya sanar da Shugaban kasan, amma hakan, daman yana kan abin da suka shawarta na yin sauye-sauye a sashen na hukumomin tsaro na kasar nan.

“Akwai wannan a rubuce, wanda kamata ya yi Shugaban kasan ya zartar da shi tun kafin ya wuce hutun na shi, amma sai Osinbajo din ne ya zartar da shawarar na su. Osinbajo, ya sanar da Shugaban kasan hukuncin da ya zartas, shi kuma Shugaba Buhari, ya amince da hakan, kasantuwan su duka biyun abu guda ne. “Shi ya sanya a lokacin da Lawal Daura ya aikata abin da ya saba wa tsarin Dimokuradiyya, sai Osinbajo din ya gayyato shi fadar ta Shugaban kasa. Lawal Daura yana zaune yana jiran a yi ma shi izinin shiga ofishin na Osinbajo ne, sai aka sanar da korar na shi. “A nan take ne aka fitar da shi waje ta kofar baya wacce mataimakin Shugaban kasan yakan fita ta cikin ta, zuwa wani gida inda aka yi masa bayanin halin da yake a cikin sa. Sam ba wata hayaniya da aka yi a tsakanin mukaddashin Shugaban kasan da kuma Lawal Daura din.

Advertisement
Click to comment

labarai