Hada Karfi Da Karfen ‘Yan Adawa Da Masu Sauya Sheka Ba Zai Dauke Hankalina Ba –Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hada Karfi Da Karfen ‘Yan Adawa Da Masu Sauya Sheka Ba Zai Dauke Hankalina Ba –Buhari

Published

on


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa hada karfi da karfe da ‘yan adawa da masu sauya sheka suka yi ba zai kawar da hankalin gwamnatinsa ga cigaba da ayyukan alherai da take yi domin cigaban Nijeriya ba.

Wakazalika shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai ga tabbatar da alkawuran da ta daukar wa ‘Yan Nijeriya a kan bunkasa tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari ya bayyana haka ne a wata liyafar cin abincin rana da ya yi wa Gwamnonin da aka zaba a tutar APC da kuma wasu ‘yan majalisa na kasa a Daura jiya Alhamis.

Shugaban dai ya ce APC ta yi wa matsalolin Nijeriya fahimtar tsaf kuma tana samun kwarin giwar shawo kansu tare da goyon bayan Nijeriya.

Sanarwar da mataimakin shugaban na musamman a bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar ta kara da cewa, “za mu cigaba da yin bakin kokarinmu a kan shugabancin da Allah ya dora mu a kai kuma muna godiya da irin goyon bayan da muke samu daga mazabu”.

Shugaba Buhari ya sake cewa babu komai a tsakaninsa da wadanda suke sauya sheka, “illa muna musu fatan alheri”.

Advertisement
Click to comment

labarai