Bikin Sallah: Gidaniyar Teku Farm Ta Raba Abinci Ga Marayu A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Bikin Sallah: Gidaniyar Teku Farm Ta Raba Abinci Ga Marayu A Kaduna

Published

on


A ci gabada shagulgulan babbar Sallah, Gidauniyar Teku dake cikin jihar Kaduna ta rabar da abinci da kudi har naira dubu dari da kuma kyauta ga wasu marayu  da iyayensu maza da suka rasu masu yin sana’ar dashen yayan itatuwa dake cikin ljihar.

Gidauniyar ta yi hakan ne tare da hadin gwaiwar  sauran takwarorinsu masu sana’ar shuka itatuwa dake a cikin jihar.

 A jawabinsa a lokacin bayar da taimakon  Shugaban Gudauniyar  Alhaji Ibrahim Salisu yace,sun bayar da tallafin ne ga iyalan marayu tara da aka barsu da yara marayu guda ashirin da daya da kuma zawara tara dake a Anguwar Kabalan Doki don tallafawa rayuwar su bisa la’akari da irin halin kuncin rayuwa da suke ciki.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da sauran Lusulmai lasu hannu da shuni dasu tallafawa marayu da marasa karfi dake cikin jihar, musamman ta hanyar daukar nauyinsu don koyon sana’anar dasa itatuwa don suma  su zamo masu dogaro da kansu.

A wata sabuwar kuwa, Malaman Majam’u dake jihar Kaduna sunyi kira ga Musulmai masu hannu da shuni mazuna jihar dasu tunada marasa galihu, ‘yan gudun hijira da kuma nakasaasu wajen taimaka masu da abinci da suttura a lokacin bikin shagulgulan Sallah babba dake ake kan ci gaba da gudanar a jihar.

Sanannen Malamin Majami’a ta Christ Ebangelical dake Sabon Tasha kaduna Fasto Yohanna Buru ne ya yi kiran a ladadin suran Malaman na Majami’un a hirarsa da manela labarai jiya Alhamis a Kaduna, inda ya yi nuni da cewar akwai bukatar a tallafa masu idan akayi la’akari da irin halin kuncin rayuwa da suka tsinci kawunansu a yau.

Fasto Buru ya kuma yi kira ga iyaye dake kasar nan dasu tabbatar da suna sanya ido akan yayansu akan irin yaran da suke yin mu’amala dasu don kada su fada hannun bata gari.

Sannane Faston ya kuma yi kira ga daukacin alumlar kasar nan,musamman wadanda ke Arewacin kasar nan dasu ci gaba da zama lafiya da junansu, inda ta yi ni.uni da cewar saida zaman lafiya ne gwamnatocin dake kasar nan zasu samun damar samar da ayyukan ci gaba da zasu inganta rayuwar alumomominsu.

Shima a sana sakin na Sallar, Sakataren kungiyar Kiristoci reshen jihar Rabaran Dakta Sunday Ibrahim ya taya almumar Musulmai dake cikin jihar murnar Sallar ,inda kuma ya yi nuni da cewar, ya kamata Musulmai da Kiristoci su san cewkr dukkan mu daga tsason Annabi Adam da matarsa Hauwa’u muka fito.

Suma a nasu sakon na Sallar Rabaran  Dabid Abaya ada kuma Jonathan kira ya yi ga Musulmai masu hali dasu tallafawa marasa galihu da abinci da kuma sittira.

Advertisement
Click to comment

labarai