Za Mu Fitar Da ‘Yan Nijeriya Daga Kangin Talauci –Osinbajo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Za Mu Fitar Da ‘Yan Nijeriya Daga Kangin Talauci –Osinbajo

Published

on


Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce, babban abin da wannan gwamnatin ta sanya a gaba yanzun shi ne kokarin fitar da ‘yan Nijeriiya daga kangin talauci.

Ya ce duk wasu shirye-shirye da gwamnatin ta sanya a gaba a halin yanzun da nufin wannan manufar ce aka tanade su.

Cikin sanarwar da mai taimaka masa a fannin yada labarai, Laolu Akande, ya fitar a ranar Laraba, ta ce mataimakin shugaban kasan ya yi wadannan kalaman ne a wajen wani taro da aka yi a karamar hukumar Bariga/Somolu, ta Jihar Legas, domin taya al’ummar yankin murnar bukukuwan Sallah a ranar Talata.

Ya ce, “Ina son na jaddada maku, duk abin da muke yi muna yin shi ne domin fitar da ku daga talauci.

“Kasarmu babba ce, akwai mutane sama da milyan 200 a cikinta, a kullum samari ake kara samarwa.

Bayan nan muna kokarin ganin mun tallafa wa duk mai yin wata sana’a, kasuwanci, makanikai da dai duk masu sana’o’i.

“Domin in kun lura da yadda gwamnatin ke tafiyar da lamurranta a baya, za ku ga duk wani kasafin kudin da ta yi, ya mayar da hankali ne ga masu kananan sana’o’i.

“Amma mafiya yawansu duk kanana ne, masu yin kananan abubuwa. Wadannan su ne wadanda ya kamata mu fi mayar da hankalinmu a kansu, domin su karfafa. In talakawa suka yi karfi, hakan zai fi ma kowa kyau.

“Shugaban kasa a kullum hankalinsa yana kan talakawa ne. Hakan ne ya sanya da muka hau mulki, muka yi shawarar mayar da hankalinmu kan wasu abubuwa kadan da za su magance matsalar rashin aikin yi. Da farko muka bullo da shirin, N-Power, domin sama wa matasa da yawa da suka kammala karatun su aikin yi.

“Mun fara ne da matasa 200,000, sannan a wannan watan ma, mun sake daukan wasu 300,000. Don haka yanzun a wannan shirin namu na N-Power, muna da matasa 500,000.

Yanzun duk kananan hukumomin kasar nan suna da matasa a cikin shirin na N-Power,” in ji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai