Yaddda Aka Yi Sallar Idi A Unguwar Mil 12 Ta Jihar Legas — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Yaddda Aka Yi Sallar Idi A Unguwar Mil 12 Ta Jihar Legas

Published

on


A cikin wannan lokaci da jama’a ke gudanar da harkokin bikin Sallar Layya na wannan shekarar, Malamai magada Annabawa da sauran shuwagabannin Al’umma ke amfani da wannan damar suke wayar wa da jama’a kai da basu shawarwarin da za su amfanesu duniya da lahira, Malam Liman Abubakar Ba’are limamin masallacin jumma’a na ‘Yan darika dake unguwar Mile 12 ta Jihar Legas ya yi amfani da irin wannan damar da ya samu a cikin wannan lokacin, Liman Ba’are ya ci gaba da nuna farin cikinsa na wannan lokaci da kuma ganin zagayowar wannan shekara ta idin Babbar Sallah ta bana sannan ya umurci al’ummar Hausawa mazauna garin Mile 12 da Jihar Legas wajan bin ummurnin shuwagabannin da suke karkashinsu ya ci gaba da cewar al’mumar Mile 12 su ci gaba da godewa Allah daya basu adalan shuwagabanni da suka rike kasuwar hannu biyu-biyu domin taimakawa kananan ‘yan kasuwa, ya ce babu shakka shuwagabanin kasuwar na iya kokarinsu wajan samun wanzar da zaman lafiya da sauran al’amuran da suka shafi kasuwar.

Alh. Dauda Tarai shugaban kungiyar masu sayar da tattasai wanda shi ne daya dagacikin shuwagabannin kasuwar kuma shiya wakilci Babban shugaban kasuwar Alhaji Haruna Mohammed Tamarke Mai dankalin turawa a wajan sallar idin bisa ga tattaki da ya yi zuwa wajan wasu al’amura da suka shafi kasuwar amma ga sakon da yabar masa domin ya shaida ma al’umar kasuwar Mile 12 ya ci gaba da cewar farko dai yana yi wa Jama’ar Mile 12 fatan alheri gaba daya da kuma basu shawara da su kara hada kawunansu domin kara samun dangan taka atsakaninsu da kuma bin dokin Jahar Legos domin kasuwar takara samun zaman lafiya sannan yamika godiyarsa ga Malamai mazauna yankin Mile 12 wajan gudanar da adduoi na musamman domin kare kasuwar daga wadansu matsalohi dake damunta da fatan bazasu gajiyaba a kan hakan.

Da yake maida nasa jawabin Sarkin Hausawan Mile 12 Alhaji Haruna Jibirin a wajan sallar idin ga Al’ummar Nijeriya da duniya baki daya ya taya ‘yan uwa musulmi murnan zagawowar wannan rana mai cike da abubuwan farinciki da fatan Allah ya maimaita mana. Sannan ya umurci Al’mumar Mile 12 dasu ci gaba da bin doka da oda na Jihar Legas da shuwagabannin kasuwar Mile 12 domin karin samun zaman lafiya sannan ya ci gaba da kira ga mahaya babura da suke zirga-zirga wajan daukar jama’a zuwa ziyarce ziyarce da suyi a hankali domin kare rayuwar jama’a. A. Muntari Jabo shugaban masu sayarda Busashen tattasai da Barko bayan yanuna farin cikinsaga wannan sallah da Al-umar Musulmi  duniya ke cigaba da nuna farin cikinsu yacigaba da yabama kungiyoyin addinin musulunci dake Mile 12 wajen taimako ga marayu da gajiyaryu a cewarsa wannan lokacin ma k ungiyar marayu ta tallafa wa marayun Mile 12 da kayan sawa na misalin dubu dari hudu da fatan Allah ya saka musu da alheri.

Advertisement
Click to comment

labarai