Kwankwaso Ya Shawarci PDP A Kan Zaban Dan Takarar Shugabancin Kasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kwankwaso Ya Shawarci PDP A Kan Zaban Dan Takarar Shugabancin Kasa

Published

on


Mai hankoron ganin ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya shawarci Jam’iyyar da ta dauki wanda zai tsaya mata ne daga sashen arewa maso yammacin kasar nan, domin ba ta daman lashe zaben ba tare da wahala ba.

Kwankwaso, ya fadi hakan ne ga wakilan taron kasa na Jam’iyyar daga Jihar Edo, jiya, gabanin zaben fidda da gwanin da Jam’iyyar ta shirya yi a watan Satumba 2018, ya kara da cewa, hakan zai baiwa Jam’iyyar daman lashe zaben bisa la’akari da yawan al’umma da suke sashen.

Ya ce, “Sanannen abu ne cewa, a bisa sakamakon kidayan da aka yi, Jihar Kano ta fi kowace Jiha a kasar nan yawan al’umma, sannan kuma yankin arewa maso yamma ya fi kowane yanki cikin yankunan kasar nan shida yawan al’umma, kana kuma, tsohuwar Jam’iyyarmu za ta fitar da dan takararta ne daga wannan sashen, don haka, ita ma PDP kamata ya yi ta fitar da na ta dan takarar daga wannan sahen.

“Ba na tantaman al’umman kudu maso kudu da na kudu maso gabas, duk suna nan a cikin Jam’iyyar PDP. Na tabbata in muka yi amfani da wannan daman a nan arewa da kuma wancan sakamakon na kudu maso yamma, tabbas PDP ce za ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019. Kwankwason kuma ya yi kira ga shugabannin Jam’iyyar da su nisanci aikata kuskuren da zai kai ga rashin nasarar Jam’iyyar a baban zabe mai zuwa.

Don haka sai ya shawarce su da su tsayar da dan takarar da suke da tabbacin zai iya kawo wa al’umma romon dimokuradiyya, ya bayyana cewa, a bisa masaniyarsa da mulki a matsayin sa na Gwamna har a karo biyu, Ministan kuma tsaro, sannan Sanata a majalisar kasa, yana da tagomashin jagorantar Jam’iyyar ta PDP da kasar nan ya zuwa ga tudun mun tsira. Ya ce a shekaru 26 da suka gabata, ya tsaya takara ne sau 15, amma sai biyu ne kadai ya sha kaye.

Kowa ma zai iya tsayawa takara ya kuma samu lashe zaben fitar da gwani, amma abu mafi mahimmanci shi ne, yanda za a lashe zaben na kasa bakidaya. Na fi kowa cancanta a cikin ‘yan takaran da suka kunno kai a halin yanzun. Na shigo PDP ne domin na kara mata kwarjini, na kuma tabbata, Kwankwaso ne kadai zai iya kawo wannan kujerar daga dukkanin Jihohin kasar nan,” in ji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai