Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Yi Barazanar Mamaye Abuja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kungiyar Dalibai Ta Kasa Ta Yi Barazanar Mamaye Abuja

Published

on


Kungiyar Dalibai ta kasa, (NANS), ta bayar da sanarwar cewa za ta shiga cikin babban shirin zanga-zanga na musamman kan rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa a tsakanin hukumar ilimin shari’a, ‘Council of Legal Education (CLE) da kuma hukumomin Jami’ar karatu daga nesa ta,  ‘National Open Unibersity of Nigeria (NOUN),’ inda hukumar ilimin ta shari’a ta ke ci gaba da kin amincewa da wadanda suka kammala karatun su a jami’ar domin daukan su a makarantun na koyon aikin lauya.

Kungiyar ta ce, za ta fara zanga-zangan ne a babban birnin tarayya Abuja, daga ranar 27 zuwa 31 ga watan Agusta, inda za ta mamaye baki dayan birnin tarayyan Abuja.

“Mun yanke shawarar cewa, ‘tura fa ta kai bango,’ don haka za mu zo mu mamaye Abuja, ba wanda zai yi wani aiki a wannan lokacin,’ in ji mataimakin shugaban kungiyar na kasa, (mai lura da harkokin waje), Mista Taiwo Bamigbade.

Kungiyar ta ce, rikicin ya yi sanadiyyar hana wa wadanda suka kammala karatun na su a Jami’ar daman shiga makarantun na koyon aikin lauya na tsawon sama da shekaru biyar.

Ya ce, a baya kungiyar ta rubuta wa Shugaba Buhari wasikar sanarwa kan mamayan da za su soma a ranar ta Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, (NAN) ya kawo rahoton da ke cewa, kungiyar daliban ta bayar da wa’adin watanni uku ga gwamnatin tarayya a ranar 23 ga watan Mayu, da ta dauki daliban Jami’ar a makarantar ta koyon aikin na lauya.

Kungiyar ta ce, “Akwai zamba da yaudara gami da cuta ga daliban da ma ‘yan adam, musamman matasa, a dauki dalibai a jami’a sannan a ba su takardun shaida na bogi, bayan sun kwashe shekaru masu yawa suna yin karatu, duk kuma da kudaden da suka kashe.

Mataimakin shugaban kungiyar daliban ya ce, kashi na farko na zanga-zangan na su za su fara shi ne na kwanaki biyar a Abuja, kashi na biyu kuma za su yi shi ne a ranar 1 ga watan Oktoba.

Kungiyar kuma ta yi nu ni da hukuncin da mai shari’a, Hilary Oshomah, na babbar kotun tarayya da ke Fatakwal ta yanke a ranar 4 ga watan Oktoba 2017, inda ta nemi da hukumomin Jami’an da kuma hukumomin hukumar ilimin da su je su sasanta.

Advertisement
Click to comment

labarai