Jami’ar OAU Ta Kori Dalibai Shida Kan Shiga Kungoyin Asiri — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Jami’ar OAU Ta Kori Dalibai Shida Kan Shiga Kungoyin Asiri

Published

on


Jami’ar Obafemi Awolowo University, (OAU) da ke Ile-Ife, a jihar Osun ta kori dalibai shida a bisa samunsu da shiga cikin kungiyoyin asiri.

Daliban da aka kora daga karatu a jami’ar ta OAU sun hada da; Onyekwusi Praise Chinemerem mai lambar karatu ASE/2014/218, Ojo Abiodun Olamide lambar izinin karatu MCB/2012/149, Ude John ASE/2015/362, Oladoye Tobi Olakunmi EGL/2014/383.

Sauran su ne; Ayeyi Damilola Ayomide mai lamba EGL/2016/075 da kuma na karshensu a jerin wadanda aka koran mai suna Dabis Jesulayomi Olakunle da ke da lambar izinin karatu EGL/2014/207.

An dakatar da su daga karatu a jami’ar ne bayan da aka gudanar da wani bincike a kansu dangane da tilasta ma wasu dalibai biyu shiga cikin kungiyar ta asibiti ba tare da son ransu ba.

A lokacin gudanar da bincike kan wannan lamarin, daliban jami’ar su 12 ne aka hannatasu ga rundunar ‘yan sandan jihar Osun domin zafafa bincike kan lamarin.

Bayan kamma gudanar da binciken ‘yan sandan, dalibai shida daga cikin wadanda aka bincika, an tabatar da sun kasance daga cikin kungiyar asiri wanda hakan ya saba wa dokoki da ka’idojin jami’ar.

Da yake tabbatar da korar dalibai shidan, Magatakardar Jami’ar ta Obafemi Awolowo, Magaret Omosule ya ce “Biyo bayan zafafa bincike kan daliban da ‘yan sanda suka yi, jami’an ta amshi cikakken rahoton da ‘yan sanda suka samar, wanda a cikin rahoton sun tabbatar da dalibai shida na jami’ar nan sun kasance mambobi na kungiyoyin asiri,” A cewarsa.

Advertisement
Click to comment

labarai