INEC Ta Shawarci Jama’ar Kebbi Kan Karbar Katin Zabe — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

INEC Ta Shawarci Jama’ar Kebbi Kan Karbar Katin Zabe

Published

on


Hukumar INEC a Jihar Kebbi ta shawarci Al’ummar Jihar kan zuwa su karbi katin zabensu ga ofisoshinsu da ke a dukkan kananan hukumomin 21 da ke akwai a cikin Jihar ta Kebbi.

Shawarar yin hakan ta fito ne daga bakin kwamnishin hukumar INEC na Jihar, Barista Ahmad Bello Mahamud yayin wata zantawa da ya yi da manema Labaru a ofishinsa da ke Birnin-Kebbi a jiya. Shugaban hukumar ya ci gaba da cewa ”A jihar Kebbi hukumarsa ta yi wa mutun 271,224 rigistar katin zabe wanda daga cikinsu 155,879 maza ne sai kuma 115,345 sune mata dukkasu daga fadin jihar ta Kebbi”.

Ya kuma cewa hukumarsa ta karbo katutukan zabe na dindindin daga babban ofishin ta na kasa kimanin 117,863 amma 40,415 ne kacal aka karba a jihar. Har ilayau ya ce” akwai sauran katutukan zabe kimanin 77,349 da ba a karba da ke a ofishin hukumar a ajiye”.

Saboda haka shugaban ya yi amfani da wannan dama domin yin kira ga al’ummar jihar ta Kebbi da duk wanda bai karbi katin zabensa ba tau ya hamzarta zuwa ofishin hukumasa da ke a kananan hukumominsa domin karba katin. Bugu da kari ya yi kira ga yaran da suka kai kimanin shekaru Goma shatakwas da suyi kokarin zuwa suyi rigistar katin zaba a ofisoshin hukumar ta INEC da ke a dukka kananan hukumomin 21 na Jihar da kuma karbar katin kafin kashen wannan watan da muke ciki.

Daga karshen ya yi godiya ga gwamntin jihar kebbi, kungiyoyi masu zaman kansu da hukumar wayar da kai da kuma ‘yan jaridu kan irin kokarinsu da suke yi kan fadakarwa game da  muhimmancin yin rigistar katin zabe da kuma karba a duk fadin jihar.

A karshe ya ce, cibiyar tana shirin yin hadin gwuiwa da ma’aikatar gona ta tarayya yadda za’ a bayar da kwarin gwaiwar fitar da kaya da kuma samar da ayyukanyi ga ‘yan kasar na.

Advertisement
Click to comment

labarai