Hukumar NAFDAC Ta Lallata Kodin Da Tramadol A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hukumar NAFDAC Ta Lallata Kodin Da Tramadol A Bauchi

Published

on


Hukumar NAFDAC ta lalata jabun magunguna da wadanda suka daina aiki harda  Kodin  harda Tramadol a  titin Bajoga dake cikin jihar Gombe da kudinsu ya kai naira miliyan 464,731,552.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar data fitar, inda tace, shugaban hukumar na shiyyar Arewa masu Yamma Sabo Adamu ne ya wakilici Darakta Janar ta Hukumar  Farfesa Mojisola Adeyeyea lokacin lalata mgungunan da jami’anta suka kwato daga gun kamfanonin da suke sarrafa su ,inda sanarwar ta kara da cewar sauran kayan  kuma masu sarrafa su ne suka kawo su don kashin kansu.

Kwamishinan lafiya na jihar Barka Sammy ne ya wakilci gwamnatin jihar a lokacin da ake lalata magungunan, inda kuma Iyan Gombe Alhaji Inuwa Lamido, ya wakilci Sarkin Gombe.

Adeyeye ta ce,  NAFDAC zataci gaba da yin dukkan mai yiwa akan yakin da take yi na sayarwa da kuma sarrafa jabun magunguna a kasar ta kuma roki yan siyasa da shugabannin alumma da masarautun gargajiya akan wayarwa da alumma kai akan jabun magunguna, musaman wadanda ake yin fasa kwaurin su zuwa cikin kasar nan.

Ta yi kira ga gwamnatin jihar ta kafa kwamitin yaki da jabun magunguna tare da sanya hukumar acikin kwamitin  da kuma sauran hukumomi makamantansu dake jihar.

Ta kuma yi kira da samar da wuri da ababen hawa ga hukumar a dukkan shiyoyyion dake fadin jihar guda uku, inda ta ce misali kamar a Kumo da Billiri don hukumar ta samu sukunin karade yankunan.

Gwamnan jihar ya umarci Janar Manaja na gidan Radiyo mallakar gwamnatin jihar da ya tattauna da hukumar akan yadda za a wayarwa da alummar jihar kai akan jabun magunguna.

Advertisement
Click to comment

labarai