Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 2 A Ranar Sallah A Ogun — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 2 A Ranar Sallah A Ogun

Published

on


Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar Ogun tabbatar da mutuwar mutane biyu a ranar Talata  a sakamakon fashewar wata tayar motar haya a kan babban titin Legas zuwa Ibadan.

Kwamandan shiyya na FRSC, Mr Clement Oladele, ya shaida wa (NAN) hakan a Abeokuta a jiya Laraba, yana mai shaida cewar hatsarin ta auku ne wajajen karfe biyar na yammaci a kan babban titin Lamona.

Oladele ya shaida cewar motar kabu-kabu kirar Bolkswagen mai dauke da lamba LSR 971 DG inda ta lodo fansonjoji  28 da suka kunshi; mata 16, maza 12 da kuma yara guda uku.

Ya shaida cewar hatsarin ta auku ne a sakamkon fashewar tayar motar, wanda hakan ya sanya motar ta dugungulen bazata.

Ya ce, “Biyu daga cikin wadanda hatsarin ta rutsa da su sun mutu, gawarwakinsu kuma an kaisu zuwa dakin adana gawarwaki da ke Isara; wadanda suka jikkata su ma an harzarta da su zuwa asibitin Isara da ke Ogere,’’ Inji shi.

Daga bisani, kwamandan shiyya na hukumar kiyaye haduran, ya shawarci direbobi da a kowani lokaci suke bin ka’idojin tuki da hukumar FRSC ta shimfida da sauran takwarorinta masu kare aukuwar hadura.

Oladele ya kuma jawo hankulan direbobi da su daina tsula gudun tsiya barkataitai a kan titinan.

Advertisement
Click to comment

labarai