Ba Zan Yi Katsalandan A Harkar Zaben Dan Takarar Gwamna Ba — Gwamna Shettima — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ba Zan Yi Katsalandan A Harkar Zaben Dan Takarar Gwamna Ba — Gwamna Shettima

Published

on


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya godewa alummar jihar a kan giyon bayan da suka baiwa gwamnatin sa har na tsawon shekaru bakwai tare da yin alkawarin ba zaiyi katsalandan ba a zaben fitar gwani na kujerar gwamnan na jamiyyar ba.

Gwamnan ya yi nuni da cewar, Allah shine yake bayar da mulki ga wanda yaso ya kuma ja kunnen wasu yan siyasa wadanda ake zargin sun wawure dukiyar jihar suka kuma mallaki jiragen sama hudu suka shigo cikin jamiyyar maici don su dorawa alummar jihar wanda zai gaje shi.

Shettima ya bayyana ha kan ne a jawabinsa a lokacin da ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki na APC dake jihar a fafar gwamnatin jihar dake Maiduguri da sukaje yi masa barka da Sallah yaci gaba da cewa,  a shekaru bakwai da suka wuce gwamnatin sa tasha fama da yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram, sake giggina matsugunan alumma da yakin ya dai-daita,giggina makarantu, samar da ababen more rayuwa, maido da martabar alummar Borno da kuma kakkafa sassanin ‘yan gudun hijira kuma ina mai godewa Allah da yau ya sake bani damar yin bikin murnar babbar Sallah daku.

Sai dai, “wannan shine karbar bakuncin ku da zanyi na karshe a matsayina na gwamna da kuma madadin gwamnagin jihar, domin wa’adina na mulki zai kare a watan Mayun shekara mai zuwa kuma ina son inyi amfani da wannan damar in roke ku ku yafe ni duk wanda na sabawa.”

Acewarsa,  “Ina kuma son ince akwai wasu ‘yayan APC da suke son sanya kiyayya a tsa kanin ‘yayan jamiyyar don manufarsu ta son rai  a kan wanda zai gaje ni, amma in Allah ya yarda baza su ci nasaraba ba domin Allah shine ke bayar da mulki.”

Ya danganta irin wadannan ‘yan siyasar a matsayin ‘yan ta’addan ‘yan siyasa wadanda kuma a lokacin da ake yaki da yan kungiyar Boko Haram suka fice daga jihar zywa Abuja da sauran wurare yanzu kuma suke son dawo jihar don karbar karagar mulki.

Gwamnan ya ce, duk wanda ya ci nasara a zaben fitar da gwani na zaben gwamna a APC a jihar zan mara masa baya.

A wata sabuwar kuwa, Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai Al Amin Elkanemi, ya kai ziyarar Sallah ga gwamnan inda ya kuma yi godiya a kan goyon bayan da masarautar take samu daga gwamnatin jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar data tarayya dasu yi dubi a kan hanyoyi daga  Maiduguri zuwa Kanwa, Malamfatori, Dikwa-Ngala-Kala Balge wadanda sun jima da lalacewa.

Da ya ke nasa jawabin, Shettima ya godewa Sarkin a kan ziyarar da kuma irin shawarwarin da yake bashi, inda  India habe tuni gwamnatin jihar ta fitar da naira biliyan daya don fara aikin hanyar Ngala- Kala Balge wacce ta hada da Kamaru kuma aikin hangar Kanwa- Malamfatori zai yi wuya a yanzu saboda aikin da soji suke yi a yankin.

Advertisement
Click to comment

labarai