An Cafke Masu Safarar Kwayar Tramadol A Jihar Kebbi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Cafke Masu Safarar Kwayar Tramadol A Jihar Kebbi

Published

on


Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta samu nasarar cafke diloli masu sayar da kwayar Tramadol a kan hanya Koko- Yauri da kuma Zuru a jihar ta Kebbi a jiya.

Bayanin hakan ya fito ne a bakin kwamishina rundunar  CP Kabiru M Ibrahim yayin wata zantawa da ya yi da ‘yan jaridu a ofishinsa da ke a Birnin-Kebbi a jiya.

Haka kuma kwamishinan ya cigaba da cewa “A ranar 29 ga watan Yuli jami’an sa sun cafke wata mota kirar Tayota mai Lamba AU10 MNN da kuma sunan direban motar Abdulwahab Salihu dauke da kwali uku na kwayar Tramadol kanya Yauri da  ke cikin jihar ta kebbi, wanda tuni rundunar ta ‘yan sanda ta hannun tawa hukumar NDLEA  ta jihar kayan laifin da kuma direban motar domin gudanar da binciken kan laifin domin hukumar ce ke da hakkin binciken irin wananan laifufuka”. Ya kuma kara da cewa “ a ranar 7 ga wata Agusta da kuma  15 sun kama Garba Musa dan kasar Nijar da kuma  wasu mutanen ‘yan kasar Najeriya  da laifin fataucin miyagun kwayoyi  zuwa cikin jihar ta Kebbi , masu laifin da ake tuhuma sun hada da Charles Ajamma, John Igweilo, Osita Nneli, Emmanuel Ohamchi da kuma Ibuka Onyema da kwali Takwas da rabi na kwayar Tramadol , Diazapam da kuma kwayar  Edetol  da akafi sani da suna “Farin Malam”.

Saboda haka dazarar  rundunar ta  kammala  nata bincike zata hannun ta masu laifin da kuma kwayoyin da aka kama ga  hannunsu  ga hukumar NDLEA domin  gabatar dasu gaban kotu. Har ilayau kwamishina Kabiru Ibrahim yace rundunar sa ta fantsama fagen kama harantatun kwayoyi ne bisa ga ummurnin  da shugaban rundunar ta ‘yan sanda na kasa ya bayar  domin ganin cewa an rage yawan aikata miyagun laifufuka a cikin kasar Najeriya. Domin  an lura da cewa mafi a kasarin miyagun laifufukan da ake aikatawa a kasar nan ya ta’alaka ne ta hanyar shan miyagun kwayoyi. Saboda haka ne ake son a rage matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jahohin kasar nan.

Bugu da kari ya yi kira ga al’ummar jihar ta Kebbi dasu ci gaba da taimaka wa rundunar ‘yan sanda da bayanan sirri domin magance matsalolin aikata miyagun laifufuka da kuma shan miyagun kwayoyin a jihar ta kebbi da kuma kasar Njeriya baki daya. Daga karshe ya godewa ‘yan jaridu masu aiki a jihar don irin kokarin da suke yi wurin ganin cewa sun yada nasarorin da rundunar ‘yan sandan jihar ke samu kan tabbatar da tsaro da kuma kare dukiyoyin al’ummar jihar da na kasa baki daya.

Advertisement
Click to comment

labarai