An Bukaci A Gaggauta Samar Da Albashi Mafi Karancin A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Bukaci A Gaggauta Samar Da Albashi Mafi Karancin A Nijeriya

Published

on


Kungiyar kwadago ta yi kira ga gwamnatin tarayya data kara zagewa akan fitar da sakamakon biyan matsakaicin albashi ganin cewar tuni ta mika rahoton ta a sati mai mai zuwa ga majalisar kasa akan sabon tsarin albashin.Ta kuma yi kira da a gaggauta tura sakamakon zuwa ga sassan gwamnatin da suka dace akan muhawa akan sabon albashin na ma’aikatan. Shugaban kungiay ta ULC, Joe Ajaero ne ya yi wannan kiran a hirarsa da wakilinmu a garin Abuja, inda ya yi nuni da cewa, tsikon da ake samu wajen shirin na sabon albashin da kuma sake sabunta shi yana sabawa dokar ma’aikatan kwadago wadda kuma ma’aikatan bas son hakan.Acewar sa, dukkan masu ruwa da tsaki sunson a sanar da dasu a bisa da’ida akan dokar dake samar da walwala a wuraren ayyukansu a kasar kuma kungiyar tana kan kara yin masin lamba akan sake sabunta yadda aka sayar da hannun jarin kamfanin samar da wutar lantarki mallakar gwamnatin tarayya, inda ya yi nuni da cewa, sake sabuntawar zata zata kawo karshen wahalar da masu yin amfani da wutar suke fama da ita musamman na rashin wutar da kamfanin rabar da wutar na Discos yake yi a daukacin fadin kasar.Yaci gaba da cewa,“muna kuma son da a gaggauta biyan hakokin ma’aikatan na tsohuwar hukumar samar da wutar PHCN, har ila yau, ma’aikatan suna bukatar Shugaba Mumaadu Buhari ya ya gaggauta sanya hannu a dokar ma’aikatar mai. Ajaero  ya nuna damuwarsa akan cewar duk da cewar dokar kudurin (PIGB) yana tafiya ne kafada da kafada da  dokar ma’aikar man duk da iya tsawon dadewar data yi a majalisar kasa har yanzu ba’a sanya mata hannu ba,muna kira ga shugaban kasa da gaggauta sanya mata hannu don ta zama doka.”

a wata sabuwa kuwa Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Ayuba Wabba, ya sanar da cewa, tura dokar ta sabon albashin da sauransu kungiyar ta damu matuka kuma zata ci gaba da jajircewa akan hakokin ma’aikatan kasar nan.

Advertisement
Click to comment

labarai