Sarkin Zazzau Ya Nemi Hada Hannu Don Yaki Da Miyagun Kwayoyi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sarkin Zazzau Ya Nemi Hada Hannu Don Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Published

on


Mai Martaba Sarkin Zazzu Dakta Shehu Idris, ya yi kira da a hada karfi da karfe don yaki da ta’ammali da miyagun kwayiyi a kasar nan, musamman a tsakanin matasa. Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar talata a lokacin da yake ya yiwa alummar masarautar jawabi da suka taro a Kofar Fada dake Zaria don gudanar bukukuwan sallah babba.  Dakta Shehu wanda kuma shune shugaban Majalisar Sarakuna da kuma na Cif-Cif, ya yi nuni da cewar kiran ya zama wajibi idan akayi la’akari da illolin na shan miyagun kwayoyin suke jefa matasa a ciki. Ya yi kira ga iyaye dasu kiyaye akan nauyin da Allah ya dora masu na talbiyar yayansu yadda zasu zamo wadanda kasa zatayi tunkaho dasu wajen ciyar da ita gaba.

Acewar sa, “ina mai kara kira ga iyaye su kara kaimi wajen ilimantar da yayansu da ilimin addini dana zamani da kuma basu tarbiyya yadda zasu zama masu amfani a nan gaba.”

Sarkin ya kara jaddada cewar,” dole ne mu sanya ido akan yayanmu gaba daya don dorasu a bisa turbar data dace ta rayuwa.” Ya kara da cewar, “ ina son inyi amfani da wannan damar don yabawa gwamnatin jihar da kuma ta tarayya akan nasarorin da suka samar a yan shekarun da suke akan karagar mulki, ina kuma kira ga alumma dasuci gaba da  baiwa gwamnatin goyon baya akan sshirye shiryen ta, musamman na inganta rayuwar alummar.”Ya kuma yi kira ga alummar jihar dasu sanar da hukumomin da suka dace in sunji barkarwar wata cuta su kuma sanar da jami’an tsaro da bayanai lasu amfani akan wani abu da basu yarda dashi ba. Sarkin ya kuma gidewa Musulmai da sauran alumma akan addu’oin da sukayi don samun zaman lafiya ya kuma roke su da suci gaba da yin addu’oin, ya kuma yi adduar Allah ya karbi ibadun mahajjatan bana da suke sauke faralin su a Saudiyya. A cikin hudubarsa tunda  farko a Masallacin Idi na Kofar Gayan Low-cost, Babban Limamin Dakta  Muhammad Aliyu, yace addinin Musulunci ya hori dukkan Musulmi ya koyi digaro da kai ya kuma ja hankalin Musulmai akan ragwancci.

Advertisement
Click to comment

labarai