Sallar Idi: Sarkin Kano Ya Gargadi Al’umma Su Zauna Lafiya Da Kaunar Juna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sallar Idi: Sarkin Kano Ya Gargadi Al’umma Su Zauna Lafiya Da Kaunar Juna

Published

on


A jiya Talata ce Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gargadi al’ummar nijeriya das u ci gaba da zama lafiya tare da kaunar juna domin tabbatar da hadin kai.

Sarkin ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kamala jagorantar sallar idin bana wadda ya yi a masallacin idi na Kofar Mata da ke cikin garin Kano.

Saboada haka sai ya bukaci dukkan ‘yan Nijeriya daga kowane bangare das u tabbatr da cewa, sun karfafa zaman lafiya a tsakaninnsu

Sannan kuma ya bukaci al’ummar jihar Kano das u ci gaba da yin addu’a samun zaman lafiya a dukkan fadin jihar da ma kasa baki daya musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar zaben shekara ta 2019.

Haka kuma sarkin ya yi addu’ar samun amfaniun gona mai albarka a wannan damuna ta bana , sanna kuam ya bukaci matasa das u tabbatar da sun samu sana’o’in da za su dogara da kansu, yadda za su bayar da gudummawar bunkasa tattalin arzikin wannan kasar.

Advertisement
Click to comment

labarai