CAN Ta Taya Musulmi Murnar Babban Sallah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

CAN Ta Taya Musulmi Murnar Babban Sallah

Published

on


Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN, ta taya al’ummar Musulmin kasar nan murnar bukin babban Sallah na wannan shekarar.

Shugaban Kungiyar ta CAN, Rabaran Samson Ayokunle, ne ya mika wannan sakon cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yada labarai, Fasto Adebayo Oladeji, ya sanya wa hannu a ranar Litinin a Abuja.

Ya kuma bukaci Musulmin kasar nan da kar su manta da sadaukarwan da ke cikin rayuwa irin ta Annabi Ibrahim, a lokutan shagulgulan na su.

Ayokunle ya ce, ya kamata Musulmin su sani cewa, ba wata sadaukarwar da ta sha karfin zaman lafiya da kwanciyar hankali, soyayya, hadin kai, yafiya da hakurin zama da juna a dukkanin alakar su da wadanda ba Musulmin ba.

“Akwai hikima a bisa yadda Allah Ya yarda da zaman mu Musulmi da Kirista a matsayin ‘yan kasa guda.

“Muna kira ga dukkanin ma’abota Addinan biyu da su rungumi junan su a bisa so da kauna da zaman lafiya.

“Da zaran mun yi hakan, kashe-kashen da ake ta yi a Nijeriya za su zama tarihi, matukar bakidayanmu, Kirista da Musulman mu za mu fahimci cewa tushen mu guda ne shi ne Babanmu Ibrahim.

“In kuwa duk mu ‘ya’yansa ne, to wace riba muke ci a wajen kashe junanmu? Ibrahim mutum ne mai son zaman lafiya mai kuma imani, lokaci ya yi da ya kamata mu yi koyi da shi, “ in ji shi.

Ya bayyana bakin cikinsa kan yadda wasu gwamnatocin arewa ke ayyana yaki da kiyayya a kan Kiristoci.

“Misali, yawancin gwamnatocin ba sa yarda su bayar da takardun mallakan filaye ga majami’u, da nufin hana su mallakan wuraren ibada, bayan kuwa tsarin mulkin Nijeriya wanda aka yi wa kwaskwarima na 1999, ya bayar da ‘yancin yin ibada ga kungiyoyi.

“Wanda lamarin ba hakanan yake ba a Jihohin da Kiristocin suka fi yawa na kudancin kasar nan. Ya zama tilas a kawar da wannan domin hadin kai da dorewar zaman lafiya,” in ji shi.

Ya ce, a bisa yadda babban zaben 2019 ke kara kusantowa, ya kamata ‘yan siyasa su daina dabi’ar siyan kuri’u, tashe-tashen hankula, zubar da jini da sauran yakin neman zabe ta hanyoyin da ba su dace ba.

Ya kuma shawarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta tabbatar duk wanda ya cancanci jefa kuri’a an ba shi damar yin rajista, ba kuma tare da wata boyayyar manufa ba.

“Abin takaici ne yadda yawancin ‘yan siyasarmu ba suna yi ne domin kishin kasa ba, suna neman shugabancin ne kadai domin su tara dukiya, wanda wannan shi ya sanya ake yin siyasan ko a mutu, ko a yi rai.

“Matukar Jam’iyyar siyasa ta yi abin da ya kamata, to ba sai ta yi amfani da karfi ko haddasa rigima ba domin ta kare kujerar ta.

“Allah Ya yi wa kasarmu jagoranci, daga dukkanin kangin da take ciki, ya sanya zaman lafiya da hadin kai a kasarmu bakidaya, ya kuma yi wa Shugabanninmu jagoranci a dukkanin matakai.”

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai