Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabanin Rundunonin Tsaro — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Shugabanin Rundunonin Tsaro

Published

on


Ranar litinin data gabata ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta sirri da Shugabanin rundunonin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja, inda bayan ya kammala ganawar ce ya wuce zuwa mahaifarsa ta Daura dake cikin Jihar Katsina don yin sallah babba a can.

A hirarsa da manela labarai dake a fadar ta shugaban kasa jim kadan bayan kammala ganawar ta sirri, shugaban rundunar rundunar tsaro (CDS), Majo Janar Abayomi  Olonisakin, ya bayyana cewar manufar ganawar itace anyi nazari ne akan lamarin harkar tsaron kasar kuma ganawar tafi mayar da hankali akan lamarin jahohin Biniwe, Zamfara da kuma Taraba.

Acewarsa, “ mun shafe awowi biyu da rabi  muna ganawa da shugaban tare da sauran shugabannin rundunonin tsaro na kasa, inda muka tattauna akan lamarin tsaro da ya shafi kasar nan baki daya.”

Ya kara da cewar, “dukkan mun tofa albarkacin bakunan mu a lokacin ganawar, musamman akan lamarin tsaro da ya shafi jahohin Biniwe, Zamfara, Taraba, shirin yaki na  Whirlstroke da kuma shirin yaki na  Saradaji.”

Ya ci gaba da cewa, “ mun sanar da shugaban kasar akan nasarorin da shirin suja samar kuma za’a ci gaba da gudanar da shirin guda biyu a bisa yadda suka dace kuma dukkan wadannan shirin biyu an tattauna akansu kuma zamu kara yin kaimi don ganin cewar mun kare kafiyar ‘yan kasar nan da kuma dukiyoyinsu .”

Shima da yake nashi tsokacin akan ganawar, Ministan Tsaro Dan Ali Monsur yace, ganawar dama an saba yinta inda ake yiwa shugaban kasa bayani akan lamarin tsaron kasar kuma karin bayani ne aka yiwa shugaban akan lamarin tsaron kasar ganin cewar ya ya bar kasar a kwanan baya.

Dan Ali ya kara da cewar,”munga kuma lamarin tsaro an kara samun ci gaba a kasar, musamman jahohin  Zamfara,  Biniwe, Taraba da kuma yankin Nija Delta sai dai a yankin.

Arewa maso Yamma, muna samun rahotannin da suke damun mu amma muna yin nazari akan lamarin don daukar matakan da suka dace.” Sauran manyan shugabannin mu tsaron da suka hallarci ganawar sun hadada; shugaban hafsan hafsoshin soji Tukur Yusuf Buratai, shugaban hafsan soji na mayakzn ruwa Ebok Ibas dana sojin sama  Sadikue Abubakar, shugaban yansanda na kasa Ibrahim Idris,  mai bayar da shawar akan fannin tsaro Manjo Janar  Babagana Monguno mai ritaya, shugaban hukumar farin kaya na DSS mai rikon kwarya  Matthew Seiyefa, Darakta Janar na (NIA), Ahmed Abubakar da kuma Sakataren gwamnatun tarayya Boss Mustapha.

 

Advertisement
Click to comment

labarai