Bikin Sallah: Saraki Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Zauna Lafiya Da Juna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Bikin Sallah: Saraki Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Zauna Lafiya Da Juna

Published

on


Shugaban Majalisar Dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi amfani da koyarwa da darussar dake tattare sallar layya wajen karfafa soyayya da juna musamman a wannan lokacin da ake gudanar da bukuwan sallah da dukkan sauran lokaci gaba daya.

Dakta Saraki ya yi wannan bayanin ne a cikin sakonsa na gaisuwar babban sallah ga al’umma musulmi na kasar nan baki daya, sakon dai ya samu sa hannun mai bashi shawara ne na musamman a kan harkar watsa labarai Mista Yusuph Olaniyonu, aka kuma raba wa manema labarai a Abuja.

Ya kuma kara yin kira garesu dasu kara kaimi wajen ciyar da marasa galihu da kuma dauriya da kuma yin addu’o’i ga Allah na neman samun nasara a dukkan harkoin da kasar nan ta sa a gaba. Shugaban majalisar dattijai ya kuma bukaci Musulmi dasu dukufa wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da hadin kai da kuma karin bunkasar tattalin arziki musamman a yayin da suka fuskanci Allah a filayen idi na kasar nan.

Ya kuma taya al’ummar Musulimi murnar bukin babbar sallah, yana mai cewar, ‘Wannan lokaci ne na komawa ga Allah kamar yadda Annabi Ibrahim ya mika wuya ga Allah ta hanyar sadaukar da dansa Ibrahim domin cika umarnin Allah.”

“Kamar yaddda muka karanta a cikin Alkur’ani mai girma, yayin da Annabi Ibrahim ke kokarin yanka dansa Isma’il, Allah madaukakain Sarki ya canza masa da rago daga gidan aljanna, a don haka ne musulmi ke amfani da wannan koyarwar wajen nuna sallamawarsu ga Allah madaukakin Sarki.” Inji shi.

Shugaban majalisar dattijan dai ya yi sallar idi ne a babbar masallacin Idi dake garin Ilorin ta jihar Kwara

Advertisement
Click to comment

labarai