Bikin Sallah: Hukumar FRSC Ta Bukaci Goyon Bayan A’lumma — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Bikin Sallah: Hukumar FRSC Ta Bukaci Goyon Bayan A’lumma

Published

on


Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, ta nemi hadin kan al’umma musamman masu ababen hawa da su bi umurnin da jami’an hukumar ke ba su da kuma dokokin sauran hukumomi.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, Dakta Boboye Kazeem, ne ya yi wannan kiran cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Kazeem ya jiyo babban shugaban hukumar na kasa, Dakta Boboye Oyeyemi, yana cewa a cikin sakon sa na Sallah, inda yake tabbatar wa da al’umman kasar nan cewa, hukumar ta yi shirin samar wa da al’umma lafiyayyun hanyoyi a lokutan na Bukukuwan Sallah da ma bayan hakan.

Oyeyemi, ya yi kira ga masu ababen hawa da su yi tuki bisa lura, su kuma nu na hakuri ga sauran masu amfani da hanyoyin domin nu na darussan da wannan lokaci na sadaukarwa ke tattare da shi.

A cewar shi, bukukuwan Sallah, al’ada ce na sadaukarwa, wanda ke baiwa Musulmi daman kara yin nazarin darajar rayuka da kuma nu na jinkai da tausayawa ga rayukan mutane wanda Allah Ya yi ta inda ya fanshi ran Annabi Ismail da rago.

Ya kara nu ni da cewa, darasin da ke cikin yanda Allah Ya fanshi ran dan Adam da Rago, hakan yana kara nu na mana darajar ran dan Adam din ne.

Daga nan sai Oyeyemi ya bukaci mutane da su guji aikata duk wani abin da zai iya jefa rayuwarsu da ta makwabtan su a cikin hadari a lokutan shagulgulan na Sallah.

Ya ce, “Mun sanya isassun ma’aikatanmu da kuma kayan aiki domin su tabbatar da lafiyan hanyoyinmu su kuma ceci masu ababen hawa a ko’ina cikin kasar nan.

“Domin samun kyakkyawan sakamako, hukumar ta umurci dukkanin jami’anta masu aiki a kan hanyoyinmu da su fi mayar da hankulansu a kan masu yin tukin ganganci, yin waya ko amsa wayan a lokutan da suke yin tuki.

“Su kuma kula da masu saba ka’idodjin hanya, yin tuki a cikin maye, yin lodin da ya wuce ka’ida da masu haska fitullun da suka wuce ka’ida da za su iya jefa sauran masu ababen hawan a cikin hadari.”

Ya kuma roki al’umma da su hanzarta kiran layukan hukumar ta wannan layin da ba a biyan ko sisi a kansa a lokutan bukukuwan, a duk lokacin da wani hadari ya auku.

Ya ce, duk layukan hukumar da sauran hanyoyin tuntubar ta za su ci gaba da kasancewa a bude a lokutan shagulgulan da ma bayan nan domin karba bukatun al’umma.

Advertisement
Click to comment

labarai