An Tsinci Gawar Yaro Bayan Cire Masa Sassan Jiki A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Tsinci Gawar Yaro Bayan Cire Masa Sassan Jiki A Bauchi

Published

on


Wasu marasa tsoron Allah da tausayi, sun yi wa gangan hallittar wani yaro dan shekara tara da ke unguwar Gudum Hauwasa a cikin garin Bauchi mummunar ta’adi inda suka ciccire masa sassan jiki hadi da yasar da shi a kufai.
Yaron mai suna Hassan Mohammed an tsinci gawarsa ce a ranar Laraba a makarantar Firamaren Gwamnati da ke Gudum Hausawa, makasan sun cire masa dukkanin idanunsa, sun kuma yanke masa dukkanin hannaye biyu, hadi da cire masa dukkanin kafafunsa, yanke masa azzaki da kuma cire masa kwakwala bayan sun fasa tsakar kayin yaron.
Wasu mazauna kauyen da muka ji ra’ayinsu, sun ce da iyuwar an ciccire sassan jikin yaron ne domin yin tsafi.
Wani ganau kuma mazaunin yankin ya ce, “Kamar yadda muka ga gangar jikin yaron bayan an gama ciran ababen da za a cire, muna tsammanin yaron an kashesa kwanaki hudu ko sama da haka ma.
“Sanna, muna kuma tsammanin yadda aka ciccire sassan jikin yaron kila za a yi tsafi ne da ababen jikin yaron,” inji shi
Ya kara da cewa; an kai ga gano gangar jikin yaron ne a lokacin da wasu yara ke gudanar da wassan kwallo a cikin filin makarantar, bayan gano ganawar an sanar da mai unguwa inda shi kuma ya sanar da ‘yan sanda domin tsamo gawar daga inda makasan suka yasar da ita.
Majiyarmu daga yankin, ta shaida mana cewar yaron yana sayar da Aware ne, inda makashin ya sayi Awaran hadi da bukatarsa da ya biyosa domin amsar kudi, inda suka kai ga ida nufinsu a kansa.
Ya ce; “Ganin karshe da yaran yankin suka yi wa mamacin, sun ganshi na kuka na bin wani mutum inda ke cewa masa ya bisa kudin Awaransa da ya ci masa.
“Abun takaici, kwanaki hudu bayan haka an yi ta neman yaron amma ba a gansa ba; kwatsam sai tsintar gangan jikinsa aka yi a yashe, bayan an yi masa mummunar kisan gilla ta rashin imani da tausayi” Inji mai bamu bayanin
A lokacin da wakilinmu ya ziyararci gidan su marigayin, ya tarar da mahaifin yaron da sauran jama’a suna amsar gaisuwar jaje cikin jimami da dimauta.
Mahaifi yaron da aka kashe mai suna Usman Fari, mai shekarun haihuwa 65, ya shaida wa wakilinmu yadda lamarin ya auku daki-daki.
Ya bayyana cewar sun kai rahoton bacewar yaronsa ga ‘yan sanda tun bayan da awa 24 yayi ba tare da ganinsa ko jin motsinsa ba, “Yarona ya tafi saida Awara, wani mutum ya kirasa ya sayi Awaran naira 20 a hanunsa, bayan da ya kammala ci sai ya tashi ya kama tafiyarsa ba tare da ya biya yaron kudin Awaran ba.
“Dana ya bisa inda ya bukaci ba bashi kudinsa da mutum ya ki biya. Ya bisa daga wurin da ya ci Awaran zuwa wani wuri da ya kai nisan kilomita biyu, har wannan lokacin mutumin nan ya ki biyan kudin nan, daga wannan lokacin babu wani mutumin da ya san meye kuma ya faru ba,” Inji Mahaifin marigayin
Usman Fari ya tabbatar da cewar yara da dama sun ganshi ‘Dansa’ a lokacin da ke bin mutumin yana neman ya bisa kudinsa, inda ya bayyana cewar yara sama da biyar sun tabbatar sun ga yaron da mutumin a lokacin da suke jani-in-jaka.
Mahaifin yaron ya shaida irin yadda suka illata yaro dan shekara tara, “Idanuwansu biyu, da kafafuwarsa biyu, hannayensu dukka, da kuma tsaka tsakiyar kansa dukka makasan sun cire. Sun kuma fasa tsakiyar kan yaron suka cire kwakwalwarsa,” Inji mahaifin cikin jimami
Ya bayyana yadda hankalinsa ya yi matukar tashi bayan ganin dansa a yadda makasan suka masa, “Hankali ya yi matukar tashi yadda na ga rashin imani muraran, an dai kashe min dan da na haifa, na kuma yi Imani Allah ne ya bani yaron nan, kuma dukkaninmu garesa za mu koma amma ban taba sauwala wa raina irin wannan abun zai faru ba,” Mahaifin ya shaida mana cikin kuka.
Malam Fari ya nemi hukumomin da abun ya shafa su yi wa Allah su binciko makasan hadi da hukuntasu domin hakan ya zama izina ga masu yunkurin aikata makamancin hakan.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ma ya kara da cewa bincikensu har ya kai cafko wasu biyu da ake zargi kan lamarin.
Ya ce, daga cikin biyun da suka kama har da wanda ya dauki nauyin irin wannan kisa da cire wa yaron sassan jiki, “Mun kama wanda ya sa da wanda aka sa,” Inji DSP Datti
“Mun kama wadanda muke zargi kan lamarin, ciki har da wanda ya sanya a hallaka yaron. Caji-ofis dinmu da ke Township sune suka samu nasarar cafkewar, amma daga baya an dawo da wadanda aka kama zuwa sashin amsar manyan laifuka CID da ke shalwatanmu domin zafafa bincike,” Inji Datti
Abubakar ya bukaci iyaye da suke sanya lura da kula a kan iyayansu sosai domin kariya daga masu kekasasssun zuciya.

Advertisement
Click to comment

labarai