An Nemi Al’ummar Musulmi Su Hada Kansu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Nemi Al’ummar Musulmi Su Hada Kansu

Published

on


A dai dai lokacin da al’ummar Musulmin duniya ke ci gaba da bukukuwan sallar layya, an bukace su dasu zama tsitsinya madaurinki daya a dukkan harkokin da za su fuskanta don samun nasarar duniya da lahira, wannan kira ya fito ne daga bakin Limanin masallacin idi na kauyen Utako dake yankin babbar birnin tarayyar kasar nan Abuja, Liman Alhaji Musa Aliyu Imam a cikin hudubar da ya yi wa  al’ummar Musulmin da suka halarci sallar idi layya jiya a filin idi na Utako.

Liman Alhaji Musa Aliyu Imam wanda ya tattauna da wakilinmu jim kadan bayan kammala sallar idi, ya yi nuni cewa, ‘Ya kama ta dukkan musulmi su kawar da banbancin siyasa dana kabilanci a tsakaninsu  su kuma dukule waje daya, ta haka ne za a samu nasarar tabbatar da zama lafiya da kwancitar hankali a kasa Nijeriya baki daya. Ya kuma bukaci jama’a su gyara halayensu, ta hanyar aikata aiyyuka na gari da neman kusanci ga Allah madaukakakin Sarki.

Ya kuma ci gaba cewa, babbar abin daya kamata al’ummar Musulmi su fuskanta a halin yanzu shi ne addua’ar neman zaman lafiya a sassan kasar nan, ya kuma yi adduar Allah madaukakakin Sarki ya zaunar da kasar nan lafiya tare da ba shugabninmu baisra da karfin gwiwar tafiya da mulkin da Allah Ya basu cikin adalci.

Da ya koma a kan babban zabe na kasa dake tafe, Liman Musa Aliyu, ya hori jama’a dasu bi dukkan dokokin da aka zayyana na harkar zaben, su kuma guji tayar da rigima, ya kuma bukaci kowa ya zabi wanda ya natsu da shi, wanda yake da yakinin zai aikin don ci gaban kasa, ya kuma yi addauar Allah Ya sa a gudanar da zabubbkan lafiya. Cikin wadanda suka halarci sallar idin a kwai nai’bin Limamin masallacin, Malam Abdulzakak da sauran al’umma maza da mata.

Advertisement
Click to comment

labarai