An Gudanar Da Sallar Idin Layya A Bauchi Lafiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Gudanar Da Sallar Idin Layya A Bauchi Lafiya

Published

on


Kamar ina a fadin kasar Nijeriya, a jihar Bauchi ma, miliyoyin musulmai ne suka fito kansu da kwarkwatansu cikin ado da kwalliya domin samun nasarar halartar sallah Idi mai raka’a biyu domin raya Idin Layya ta wannan shekarar.

Wakilinmu na jihar Bauchi wanda ya baza kunnensa a kowace lungu da sako na jihar ya shaida mana cewar an gudanar da sallar Idin cikin annashuwa da kwanciyar hankali ba tare da wani firgicin da ka iya daga wa massalatai hankali ba.

Tun wuraren karfe bakwai na safiyar jiya Talatar ne dai aka fara samun massalatai daban-daban na Idi suna gudanar da sallar mai ra’aka biyu, amma a babban massalacin Idi da ke Bauchin an gudanar da sallar ne da misalin karfe tara na safiyar ranar.

Dandazon jama’a ne suka yi layi hadi da samun jam’in sallah mai raka’a biyu. Malam Bala Ahmad Baban Innah shi ne ya jagoranci gabatar da sallar Idi na bana, inda aka samu halartar dandazon, Sarakuna, Limamai, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da dukkanin rukunin al’umma kama daga maza, mata, yara da kanana dukkaninsu sun hallata domin samun jam’in Idi mai raka’a biyun.

Wakilinmu da ya kasance a filin Idin ya shaida mana cewar, Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu ya sha kwalliya da alkebba da rawani, cikin  fararen kaya yana kalliya dukka domin murna da wannan ranar ta babban Sallah, bayan gabatar da salla mai raka’a biyu, Limamin Bauchi ya gabatar da Hudubar Sallar Idi, inda daga bisani kuma Sarkin Bauchi ya yanka Ragon Laihiyarsa da kansa.

A cikin hudubar da ya gabatar, babban Limamin Bauchi, Malam Bala Ahmad Baban Inna ya shaida cewar, sunnar Layya takan hau kan mai hali, inda ya bayyana cewar babu wajibi akan dukkanin mutumin da baida zarafin yin Layyar, kana ya kuma jero irin kalar dabbobin da aka umurci a yi Laihiya da su.

Ta bakinsa, “Layya sunnah ce ga wanda ke da ikon yi, ba ce dole wanda baida halin yi sai ya yi ba, ba ce ka je ka ci bashi ko ka yi roko domin yi Layya ba.

“Ana yin laihiya da Ragon da ya kai shekara daya, Awaki kuma duk wanda ya cika shekara ya shiga ta biyu, Rakumi ana layya da wanda ya kai shekara shida ne da Shanu kuma wanda ya kai shekaru uku. Shi Layya ba a yi sai da dabbobin gida, ba a Laihiyya da tsuntsaye komai girmansu, da sauransu,” Inji Baban Innah

Limamim ya bayyana cewar yi Layya da Rago ya fi kowace dabba lada, yana mai cewa a Hadaya kuma manyan dabbobi sun fi lada domin a hadaya ana son yawan nama ne, kana ya kuma karantu sauran rabe-raben Layya, har ma ya ce ana son dukkani mai yin layya ya yanka dabbarsa da hanunsa.

Limamim na Bauchi ya kuma yi amfani da Minbarin hudubar wajen jawo hankulan jama’a kan ababen da suka kamata domin kyautata zamantakewa.

Ya kuma karanto sakon Sarkin Bauchi, da cewa “Maimartaha Sarkin Bauchi yana godiya wa dukkanin jama’a a bisa addu’o’in da ake yi wanda shi ne dalilin wanzuwar zaman lafiya da jihar nan ke dashi. Sarki na kuma rokon wadannan addu’o’in walau a daidaitu ko a jama’u a daure a ci gaba da yi domin wanzuwar zaman lafiya a jihar nan da kasa baki daya,” Kamar yadda ya karanto sakon Sarkin

Baban Innah ya kuma shaida cewar Sarkin na Bauchi yana kuma kiran jama’a da su tabbatar da yin zaben da ke tafe cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba, “kada a ci mutuncin kowa, kada a kashe rayukan kowa, kada a ji wa kowa ciwo a lokacin da ake gudanar da zaben da ke tafe,” A cewarshi

Limamim ya kuma bukaci dukkanin mutumin da ya ga ana aikata wani sabo da cewar ya tsawatar domin rage yawaitar aiyukuwar laifuka, yana mai ana samun masu yawaitar aikata Liwadi da zinace-zinace a jihar wanda a cewarsa bai kamata hakan yana faruwa ba domin kaucewa fushin Allah.

Sannan kuma Sarkin Bauchi ya kirayi gwamnatoci da su tabbatar da samar wa samari aiyukan yi wanda a cewarsa hakan zai kai ga rage yawaitar aikace-aikacen ta’addanci a fadin kasar nan.

Limamin ya bukaci jama’an jihar da su mallaki katin zabensu domin samun zarafin zabin wanda suke so, kana ya kuma nemi gwamnati ta samar da doka kan bangar siyasa domin kare jama’a, “Muna rokon gwamnati ta samar da doka wanda zai yi maganin bangar siyasa, domin duk abun da kake so ka so wa dan uwanka, wadanda yaranmu suke yi musu bangar siyasa ba zaka taba ganin ‘ya’yansu a lokadin bangar siyasa ba. Don haka talakawa suna rokon gwamnati da ta sanya dokar hana bangar siyasa,” Inji Ahmad

Limamin nan ya kuma nemi gwamnati da ta ci gaba da baiwa sashin Shari’a fifiko domin ci gaba da hukunta masu aikata munanan laifuka.

 

Advertisement
Click to comment

labarai