An Gargadi Mutane Kan Yiyuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Gargadi Mutane Kan Yiyuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa

Published

on


Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga al’umma wadanda suke zaune kusa da kogin Kaduna da su lura, saboda akwai yiyuwar ambaliyar ruwa ranar Talata da dare, ko kuma wasu kwanaki masu zuwa, saboda akwai yiyuwar karuwar ruwan sama. Malam Abdullahi Rigasa Janar Manaja na hukumar kiyaye muhalli ta Kaduna, shi ne wanda ya bayyana haka a Kaduna ranar Talata.

Kamar yadda ya kara jaddawa cewa ba wata maganar kwanciyar hankali, ga mutanen da suke zama kusa da kogi, saboda tuni dai  shi kogin ya ma riga ya cika, ruwan ma ya fi karfin wurin.

Kamfanin dillancin labarai nan Nijeriya ya bayyana ita hukumar KEPA ta ja kunnen mutane, akan yiyuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi biyar na jihar Kaduna, wadannan wuraen su ake sa yiyuwar samun ambaliyar ruwan.

Kananan hukumomin sun hada da Igabi Kaduna ta Arewa sai Kaduna ta Kudu ga Soba da kuma Kaura, don haka ya yi kira da al’ummar da suke zaune a kananan hukumomin  su kasance, a cikin zama na shirin kota kwana.

Rigasa ya kara bayyana ayyukan hukuma sun hada da ta hana aukuwar ambaliyar ruwa, da kuma tabbatar da  su mazauna kusa da wuraren suka cikin shirin kota kwana.

“Shekarar data wuce an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi goma sha hudu amma kuma ba a samu rasa rai ba”.

Ya yi kira da mazauna wuraren da su dauki wasu matakai wadanda suka hada da, gyara magudanar ruwa, da kuma su guji yin duk wani abinda ka iya toshe hanyoyin ruwa.

Ya kara yin kira ga hukumomin da suke da ruwa da tsaki akan al’amari da ya shafi gaggawa da su, shirya masu, saboda ai komai yana iya faruwa.

Advertisement
Click to comment

labarai