Amurka Ta Dora Alhakin Kashe-kashe Kan Rashin Bin Doka A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Amurka Ta Dora Alhakin Kashe-kashe Kan Rashin Bin Doka A Nijeriya

Published

on


Kasar Amurka ta dora laifin yawaitan kashe-kashen da ake yi a yankunan tsakiyar arewacin kasar nan da ma arewacin na kasar nan a kan yanda ake yi wa doka hawan kawara.

Gwamnatin ta Amurka ta ce, kashe-kashen suna karuwa ne kan gazawar da aka yi na ladaftar da masu aikata su.

“Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta karfafa dokokin ta, ta yadda za ta iya hukunta makasan,” hakanan gwamnatin ta Amurka ta bukaci Shugaba Buhari da ya tabbatar da an yi zabe na gaskiya kuma lami lafiya a babban zabe na 2019.

“Muna sa ran ganin ba a sami tashe-tashen hankulan da aka samu ba a watannin baya a lokutan zaben.

Mataimakin Jakadan a ofishin jakadancin na kasar Amurka ne, Dabid Young, ya bayyana wadannan ra’ayoyin cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi a Jos, bayan fitowarsa daga Coci.

Young, wanda yana daya daga cikin shugabannin Cocin, ‘Methodist Church,’ na Amurka, yana amsa tambayoyi ne kan mafita a rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci, ya ki cinyewa a Jihar ta Flatau, bayan da ya yi wani jawabi mai taken, ‘Libing as a Christian in a multi-religious and multi-cultural contedt.’

Ya kuma yi gaisuwa da jinjina ga Limamin kauyan Naghar, da ke gundumar Gashish, Alhaji Abubakar Abdullahi, mai shekaru 83, wanda ya bayar da mafaka ga Kiristoci a lokacin da makiyayan suka kawo masu farmaki a ranar 24 ga watan Yuni.

Mukaddashin jakadan na Amurka, ya isar da ta’aziyyar gwamnatin shugaba Donald Trump, ga iyalan wadanda aka kashe a sakamakon hare-haren na makiyaya, wadanda suka farmaki wasu al’ummu a karamar hukumar Barikin Ladi, ta Jihar.

Ya ce, “A madadin gwamnatin Amurka da al’ummar Amurka, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe a yankunan tsakiyar arewacin Nijeriya da Jihohin arewa maso yamma na Nijeriya. Mutane da yawa sun mutu, lamarin bai yi kyau ba. Muna son kara tabbatar da alfarman duk wata rai da aka kashe, ba tare da la’akari da wannan ran ta Kirista ce ko ta Musulmi ba, ko kuma ta Birom, Manomi ko Makiyayi ba.

“Ina jin a sarari yake, mun sani gwamnati ma ta sani. Mutane masu yawa suna yin abubuwa masu kyau suna kuma aiki tukuru. Amma akwai bukatar kara sanya himma domin a sarari yake akwai mutanan da dokoki ba sa yin aiki a kansu. In har mutane za su aikata manyan laifuka, ba tare kuma da an hukunta su ba.

“Yana da mahimmanci a tabbatar da an hukunta masu aikata laifukan, kan abin da suka aikata. Hakanan yana da mahimmanci a magance abubuwan da kan janyo tashin hankulan, a yaki talauci a samar da ayyukan yi, ta yadda za a taimaka wa matasa, domin tabbas matasan ne ke fadawa cikin mugayen kungiyoyi.

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai