Tambuwal Ga Tinubu—Zan Iya Takara Da Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Tambuwal Ga Tinubu—Zan Iya Takara Da Buhari

Published

on


Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya ce, in har yana da bukata, zai iya yin takarar neman shugabancin kasar nan tare da Shugaba Buhari, a karkashin tutar Jam’iyyar APC, domin yana da duk abin da ake bukata na ya yi hakan.

Gwamna Tambuwal ya fadi hakan ne cikin martanin da yake mayar wa kan sanarwar da Tinubu din ya fitar kan ficewar sa daga Jam’iyyar ta APC mai mulki.

Cikin sanarwar da ta fita a shafin Twita na gidan gwamnatin ta Sakkwato mai adireshin, ‘@sokotogobthouse,’ Tambuwal cewa yake yi, “In har da na so, in kuma da a ce Shugabancin shi ne a gaba na kamar yadda Tinubu yake zaton shi ne dalilin ficewa ta daga Jam’iyyar ta su, zan iya yin takara da Buharin, a kuma karkashin tutar ta APC. Domin ina da duk abin nema na yin hakan.”

“Tinubu ya so ya bata tafiyar ne a lokacin da aka hana shi daman yi wa Buhari mataimaki. Don haka yake zaton kowa ma hakan yake.

“Duk da hakan dai, a nan Tinubun yana kokarin nu na mana ne cewa, ba za a yi zaben fitar da gwani na gaskiya ba a cikin Jam’iyyar ta APC, wannan ya nu na babu dimokuradiyya kenan a cikin Jam’iyyar domin an hana wasu mutane ‘yancin su na dimokuradiyya.”

A ranar Lahadi ne, Tinubu ya yi zargin cewa, Tambuwal yana kwadayin zama Shugaban kasa ne.

“Dalili guda ya sanya Tambuwal ficewa. Yana kwadayin shugabancin kasa ne. Sai dai, ba shi da kwarjinin tsayawa takarar fitar da gwani da Buhari. Sannan kuma ya damu da ganin cewa, hatta takarar gwamna ma, sai an yi zaben fitar da gwani tukunna kafin in ma zai samu sake komawa,” duk in ji Tinubu, cikin sanarwar da shi da kansa ne ya sanya mata hannu a ranar Lahadi mai taken, “Sun fita ta can, mu kuma mun bi ta hanya madaidaiciya.”

Ganduje Ya Raba Tallafin Jari Ga Matasan Kano

Gwamnan Kano Dakta. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci raba tallafin jari ga matasa 8500 wanda aka ba kowanne su jarin naira 20,000 kowannen su wanda aka zabo daga kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano a karkashin shugabancin Hon. Murtala Sule Garo na ma’aikatar kananan hukumomi da al’amuran masarautu na Jihar Kano.

Gwamna Ganduje wanda ya bayyana cewa matasa da mata an basu wannan tallafin ne domin yaki da talauci da kuma bunkasa tattalin arzikin kano da kasa baki daya su dai matasan da aka bawa 20,000 kowannensu an gabatar da taron ne a gidan gwamnatin kano a ranar Asabar da ta gabata. yayin da matan su 6500 aka raba musu Naira 15000 kowaccen su a Ranar Lahadi inda Gwamnan ya ce an kashe zunzurutun kudi Naira 99,000,000.00 domin dai inganta rayuwar mata da matasa a jihar kano haka kuma Gwamnan yayi alwashin bada Naira 30,000 ga kowacce mace idan ya dawo karo na biyu a cewar Gwamna Ganduje.

Ita kuwa kwamishiniyar al’amuran mata ta Jihar Kano Hon. Hajiya ‘Yar Dada Mai Kano ta ce wannan rana ce ta mata kuma bata san abun da zata ce da gwamna ba sai dai Allah ya tabbatar mana da Alkhairin sa. Ita kuwa shugabar matan Jamiyyar APC  mai kula da shiyyar arewa maso yamma Hon.  Hajiya Yahanasu Buba ta bayyana cewa tsakanin su da gwamna ganduje sai godiya kuma su mata masu rike amana ne kuma masu rama biki ne a duk lokacin da aka musu. Ita ma shugabar jam’iyyar APC ta kano Hajiya ‘Yar Dalla ta ce su sun san irin aikin da Ganduje zai yi ma kano shi ne ma yasa suka tsaya suka yi tallan Gwamna Ganduje tun a 2014 ba tare da jin tsoron kwankwaso ba kuma ko a lokacin da ta fara tallan Ganduje kwankwaso bai hana ta ba to yau dai gashi mutanen kano na cin gajiyar aiyyukan Alkhairi na Gwamnatin Ganduje Shi kuwa shugaban karamar hukumar Dawakin Kudu wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Alhaji Yakubu Musa Naira yace gwamna ganduje da kwamishna Kananan Hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo da sauran masu taimakawa ganduje a kowanne mataki sun cancanci yabo ko da yaushe. In da mai bawa gwamnan kano shawara Alhaji Tukur Gadanya yace Ganduje goyon  Marigayi Rimi ne don haka ba mamaki a duk wani aiki da aka yi don ci gaban Kano.

Advertisement
Click to comment

labarai