Sanata Adamu Ya Bukaci A Binciki Saraki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sanata Adamu Ya Bukaci A Binciki Saraki

Published

on


Sanata Abdullahi Adamu, (APC-Nasarawa), ya yi kira da a yi binciken duk yanda aka kashe kudaden da Majalisar ta Dattijai ta karba.

A ranar Lahadi ne Sanata Adamu ya yi wannan kiran cikin wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya ce yin wannan kiran ya zama tilas in an yi la’akari da kin da Shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya yi na ya sauka daga kan kujerar da yake a kai, bayan ficewar sa daga Jam’iyyar APC, inda ya koma Jam’iyyar PDP.

Abdullahi Adamu ya ce a sarari yake, dagewar da Saraki ya yi na kin sauka daga kan kujerar yana nu na cewa akwai wani abin da yake kokarin boyewa ne.

Da yake amsa tambaya kan kiran da Jam’iyyar APC ta yi wa Sarakin na ya sauka daga kan kujerar da yake kai, Adamu cewa ya yi, “Ai a sarari yake, duk wata martaba da Sarakin yake da ita a Majalisar ta dushe kwata-kwata.

“Don ya rasa daraja da kima a wajen yawancin wakilan majalisar da dukkanin ‘yan Nijeriya na kwarai, yana dai jingine da kujerar ce kawai wacce take ba shi kariya.

Kan ko wa yake ganin zai gaji Sarakin idan da har zai yanke shawarar sauka daga kan kujerar, Adamu ya ce, “Ai ba ka tsallake gada har sai ka kai inda gadar take tukunna.

Duk kokarin da muka yi na jin martani daga ofishin shugaban majalisar ta dattawa bai yi nasara ba.

Kiraye-kirayen da muka yi ta yi a wayar mai taimaka masa kan harkokin manema labarai, Mista Yusuf Olaniyonu, ya nu na wayar a kashe take. Har yanzun kuma muna sauraron amsa ne kan sakonnin da muka aike masa ta wayar sa.

Advertisement
Click to comment

labarai