‘Nijeriya Ba Ta Gama Farfadowa Daga Matsalar Tattalin Arziki Ba’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

‘Nijeriya Ba Ta Gama Farfadowa Daga Matsalar Tattalin Arziki Ba’

Published

on


Babban mai bin diddigin lissafi na kasa, Yemi Kale ya ce, tattalin arzikin kasar nan bai farfado daga matsin tattalin arzikin da ya fada tun a shekarar 2016 ba.

Kale, wanda har ila yau shi ne shugaban hukumar bin diddigi ta kasa ya ce, rigingimun makiyaya da manoma, ya dankwafar da tattalin arzikinmu a zango na farko na shekarar 2018.

Kamar yadda rahoton tashar yada labarai ta, ‘Cable,’ ta nu na a cikin labaran ta, babban mai kididdigan na tarayya, ya yi jimamin halin da tattalin arzikin na kasar nan ya shiga a zango na biyu na wannan shekarar.

Ya ce, “Ba zan gaya maku ainihin yanda lissafin yake ba, saboda ba a kammala aikin ba tukunna, amma daga abin da nake iya gani a gabana yanzun haka, tabbas maganan hakanan take.

“Abin mamaki, amma daga abin da nake tsammani lallai lissafin zai iya fin haka kyau, lissafin ya yi kama da na zangon farko. Ina ganin har yanzun dai tattalin arzikin yana nan yana ta fama a cikin halin matsin da yake a ciki, kamar haka lissafin yake nu na wa. Misali, an sami matsaloli a fannin noma saboda rigingimun da suke ta faruwa a sassa daban-daban na kasar nan. Tabbas, in har mutane ba su yi noma ba, dole ne a sami matsala.

“Noma ba samar da hatsi ne ba kadai, a lokacin da ka lalata filayen noma, ko ka halaka shanu, wanda su ma duk suna cikin ma’anar noma, duk hakan yana kawo cikas a fannin na noma da kiwo, wanda sune manyan abin da ke bunkasa tattalin arzikin namu, matsala a cikin su kuma shi ke dankwafar da tattalin arziki..”

Kale ya ce, sanya kudaden da hukumar bayar da lamuni ta duniya ta yi a cikin tattalin arzikin namu, da nufin bunkasa shi da kashi 2.1 ya zuwa karshen shekarar 2018, hakan zai iya tabbata.

Ya kuma yi tsokaci kan jadawalin da sashen kwararru kan tattalin arziki suka fitar kwanan nan, yana mai cewa, bai dace a ce Legas tana a wannan matsayin ba.

Irin wannan jadawalin yana amfani da wani ma’auni ne kamar na Ilimi da Lafiya, wanda duk suna da matsala a Nijeriya, a cewar shi.

Advertisement
Click to comment

labarai