Gwamnan Bauchi Ya Biya Albashin Watan Agusta Don Gudanar Shagulgulan Sallah — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnan Bauchi Ya Biya Albashin Watan Agusta Don Gudanar Shagulgulan Sallah

Published

on


Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya biya ma’aikatan jiharsa albashinsu na watan Agustan nan domin tabbatar da walwala da kuma ganin an gudanar da bukukuwan sallah cikin annashuwa da kwanciyar hankali.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru wacce Kakakin gwamnan, Ali M. Ali ya sanya wa hanu hadi da raba wa ‘yan jarida a jiya 20/8/2018 a birnin na Bauchi, inda ke bayanin cewar gwamnan ya yi hakan ne domin tabbatar da jama’an jihar sun samu walwala ta fuskacin samun kudaden riritawa a yayin bukin na sallah babba.

Ya ce; “Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya amince da biyan albashin watan Agustan domin ma’aikata da wadanda suke dogaro da su samu zarafin gudanar da shagulgulan babba Sallah cikin annashuwa da wadata,” Inji M. Ali

Sanarwar ta kuma kara da cewa, gwamna M.A ya amince da biyan albashin ne tun a makon jiya gabanin ya sanya kafa ya fice daga jihar domin tafiya kasa mai tsarki don gudanar da Ibadar Hajji na bana, “Tun a makon jiya ne gwamna Abubakar ya amince da biyan albashin watan Agustan gabanin ya tafi kasa mai tsarki domin gabatar da Ibadar Hajji; tunin kuma albashin nan ya fara shiga hanun ma’aikata a karshen mako,” A cewar sanarwar

Gwamna ya kuma jawo hankalin jama’an musulmai da su kasance masu daukan darussan da suke cikin wannan Ibadar domin kyautata zaman takewa a kowani bigire, “Sannan kuma Gwamna Abubakar yana taya illahirin ‘yan Nijeriya musamman musulmai murnar zagayowar wannan Idi babba, sannan ya kuma bukaci musulmai su dauki darussan da suke cikin Layya da sadaukawar da ke tattare da Layya,” Kamar yadda sanarwar ta shaida

Ali Muhammad Ali ya kuma shaida cewar gwamnan ya bukaci illahirin ma’aikatan jihar da su tabbatar da dawowa bakin aikinsu a kan lokaci da zarar hutun sallar ta kai ga karewa domin ci gaba da yi wa jama’an jihar aiki tukuru.

GMA ya kuma yi addu’ar Allah sanya a yi hajji karbabbiya da kuma addu’ar Allah dawo da alhazanmu gida lafiya, kana ya kuma bukaci alhzzai su yi wa jihar Bauchi da kasa addu’a domin samun kyakkyawar zaman lafiya da ci gaban kasa.

Advertisement
Click to comment

labarai