Bikin Sallah: ‘Yan Sanda Sun Shirya Tsaf’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Bikin Sallah: ‘Yan Sanda Sun Shirya Tsaf’

Published

on


Sufeton ‘yan sanda na kasa, ya yi umurni da a tura jami’an ‘yan sanda a dukkan sassan kasar nan domin tabbatar da yin bukukuwan Salla lami lafiya.

Babban Sufeton, Ibrahim Idris, ya bukaci dukkanin Kwamishinonin ‘yan sanda da jami’an su da ke sassan arewa maso gabashin kasar nan da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana.

Cikin sanarwar da Kakakin rundunar na kasa, Jimoh Moshood, ya fitar yana cewa, “Su kasance a ko’ina domin su karfafa tsaro, su tura jami’an ‘yan sanda a ko’ina domin su yi sintiri, su lura da tarukan jama’a, su bayar da cikakken tsaro a filayen Sallar Idi da sauran wuraren da za a yi shagulgula, a yankunan da ke karkashin ikon su.

 “Karin ‘yan sandan da za a tura da kayan aikin ganowa da hana ayyukan barna duk za a yi hakan ne domin a gano wuraren da batagari da sauran mabarnata ke boyewa musamman a wuraren gine-ginen da ba a kammala su ba. Wadanda yawanci a nan ne batagarin ke samun boyewa da aiwatar da ta’addancin na su.

Za a ci gaba da ayyukan kawar da batagarin ne a duk tsawon lokacin da za a kwashe ana shagulgulan Sallan da ma bayan hakan. Wannan aikin kuma zai hada har da wuraren shakatawa da dukkanin wuraren taruwan jama’a da mahimman wurare da kadarorin gwamnati.

An kuma tura jami’an kula da lafiyar hanyoyi da na kiyaye hadurra da na masu hana aikata laifuka a kan dukkanin manyan titunan mu domin su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin matafiya da sauran masu amfani da hanyoyin a tsawon lokutan Sallan da ma bayan nan.

An kuma gargade su da su kasance masu kiyaye dokar aiki su kuma kasance abokanai ga al’umma na kwarai, su kuma yi da gaske wajen gudanar da aikin na su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai