ARFAH: Hukumar NAHCON Ta Shirya Wa Nijeriya Addu’a Ta Musamman — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

ARFAH: Hukumar NAHCON Ta Shirya Wa Nijeriya Addu’a Ta Musamman

Published

on


A jiya ne dandazon ‘yan Nijeriya da suka yi dafifi a filin Arfah suka gudanar da wata addu’a ta musamman ga kasar don dawwamar zaman lafiya da yalwar arziki tare da samun nasarar gudanar da zaben 2019 ba tare da wata tangarda ba.

Hukumar Kula da Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ce ta shirya wannan gangami na addu’a a filin Arfah. Inda ‘yan Nijeriya suka yi cincirindon halarta kwansu da kwarkwata. Kamar dai yadda alkalumma suka nuna, sama da ‘yan Nijeriya 55,000 ne Allah ya fuwace wa zuwa kasa mai tsarki don sauke farali a hajjin bana.

Taron addu’ar wanda Hukumar ta yi wa take da ‘Addu’ar Hadin Kai’, ya wakana ne bisa jagorancin malaman addinin Musulunci, wadanda suka fito daga shiyyoyi shida da ake da su a Nijeriya.

Malaman sun yi addu’o’i da dama na rokon Allah ya kawo karshen annobar ‘yan ta’adda da rikicin Makiyaya da Manoma a Nijeriya. Haka kuma sun yi rokon Allah ya sa a gudanar da zabukan shekarar 2019 lafiya.

Yayin bude taron addu’ar, Shugaban hukumar NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed ya ce, addu’ar ta wannan shekarar an shiryata ne da zimmar yi wa Nijeriya addu’a ganin zabe ne ke fuskanto mu.

Ya ce, muhallin Arfah wuri ne na musamman da ake amsan addu’o’i, saboda haka ne ma ‘yan Nijeriya ke da bukatar zage damtse wurin yiwa Shuganninsu addu’a, da kawunansu da kuma zabe mai zuwa.

Daga cikin manyan mutanen da suka samu halartar wannan addu’a akwai Ambasadan Nijeriya a a Saudiyya, Mai Shari’a Muhammad Dodo; Jakadan Tuntuba na Nijeriya a Jeddah, Ambasada Muhammed Yunusa, ‘yan majalisa da sauransu.

Advertisement
Click to comment

labarai