An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Kashe Matarsa Saboda Naira 1000 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Kashe Matarsa Saboda Naira 1000

Published

on


Mai Shari’a, Ntong Festus Ntong, na babbar kotun Jihar Akwa Ibom da ke zaman ta a karamar hukumar Ikot Ekpene, ta yanke hukunci a kan shari’ar wani magidanci da aka gurfanar bisa zarginsa da kisan matarsa mai dauke da juna biyu, shekaru hudu da suka gabata .

Kotun ta yanke wa magidancin mai ‘ya’ya 7, Friday John Uko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan gamsuwa da tuhumar da ake yi masa na zargin kisan matarsa Patience.

Alkali Ntong ya umarci a rataye Mista Uko, dan asalin karamar hukumar Ikot Ossom ta Jihar Akwa Ibom, har sai ya mutu, a matsayin hukuncin laifin da ya aikata tun watan Agusta na shekarar 2014.

Kotun ta yarda cewar, Mista Uko ya bugi matarsa da kafa a ciki, yayin da take dauke da juna biyu a karo na takwas bayan aurensu, lamarin da ya jawo mata ballewar jini da ya zama silar mutuwar ta.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewar, takaddama ta barke tsakanin Uko da marigayi ya Patience, bayan ta dauki kudi, N1,000, a aljihun rigarsa domin dafa abincin da za su ci a gidan.

Da yake yanke hukunci a ranar juma’a, Alkali Ntong, ya bayyana fushinsa kan yadda Mista Uko ya kashe matarsa mai juna biyu, da ya kama ta take lalabe aljuhunsa  kan Naira 1,000. Alkali Ntong ya kara da cewa, “Shari’ar ba wata mai sarkakiya ko daure kai ba ce, tunda shi Mista Uko ya furta da bakinsa cewar shi ne ya jawo mutuwar matarsa saboda sabanin da ya shiga tsakaninsu a kan N1,000.”

Advertisement
Click to comment

labarai