Kotu Ta Bayar Da Belin Dan Jaridan Premium Times — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Bayar Da Belin Dan Jaridan Premium Times

Published

on


Wakilin kafar sadarwa ta Premium Times Samuel Ogundioe wanda ya kasance a gargame tun a ranar Talata ya samu ‘yanci ta hanyar beli a ranar Juma’ar da ta gabata.
Dan jaridan Mista Ogundipe ya samu ‘yancinsa ne a da safiyar Juma’ar biyo bayan sakeshi ta hanyar beli da Alkalin kotun Majistiri mai lamba ta daya da ke Kubwa, Abuja Abdulwahab Mohammed ya yi; biyo bayan shigar da takardar neman belin daga lauyan kariya ga dan jaridan.
Gabanin samun belin na wakilin kafar, Lauyan ‘yan sanda ya yi kakkausar suka kan bukatar bayar da belin dan jarida daga lauyan da ke kareshi.
Daga karshe dai Alkalin kotun Mista Mohammed ya bayar da belinsa kan kudi naira dubu dari biyar da kuma samar da wani nagartaccen mutum da ke kusa da kotun wanda zai tsaya masa kan cike sharadin amsarsa a matsayin beli.
Bayan cike sharudan da kotun ta gindaya, Mista Samuel Ogundipe ya samu ‘yancinsa inda ya fita daga cakwamar ‘yan sanda.
Shi dai Samuel ya fada hanun ‘yan sandan ne tun a ranar Talata makon jiya a sakamakon wani rahoton da ya wallafa wanda ‘yan sanda suka nemi ya bayyana madogararsa amma ya tike kasa ya ce atafau ba zai bayyana madogararsa ba, wannan lamarin ya janyo kiranye-kiranye ga ‘yan sandan na su gaggauta sake dan jaridan, ciki kuwa har da kungiyar kare hakkin dan adamta ta Amnesty International.

Advertisement
Click to comment

labarai