Asibitin ‘ABUTH’ Zariya Zai Fara Fidar Zuciya Ta Farko A Nijeriya -Farfesa Adamu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Asibitin ‘ABUTH’ Zariya Zai Fara Fidar Zuciya Ta Farko A Nijeriya -Farfesa Adamu

Published

on


Yanzu haka mahukumtan asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,sun kammala duk shirye –shiryen da suka kamata, domin fara fidar zuciya na farko a Nijriya, domin kawo karshen matsalolin da ma su dauke da wannan cuta ke fuskanta. Mataimakin babban daraktan asibitin, Farofesa Adamu Ahmed ya shaida wa wakilinmu haka a zantawarsa da ya yi da mataimakin daraktan a asibitin da ke shika a Zariya.
Farofesa Adamu Ahmed ya ci gaba da cewar, wannan babban aiki da mahukumtan asibitin za su fara na fidar zuciya, anyi duk tanadin na’u’rorin da suka kamata, da za su tallafa wa duk wanda za a yi ma sa fidar, wadanda za su tallafa ma sa wajen yin numfashi, kafin kamala fidar da za a yi wa marar lafiyar.
Sai dai kuma Farofesa Adamu ya yi amfani da wannan dama, na yin kira ga ma su hannun – murza zare da suke da kudurin tallafa wa al’umma, da su bayar da tallafin kudi ga ma su dauke da wannan cuta ta zuciya, domin su amfana da wannan aiki da za a fara a a watan Satumbar wannan shekara ta 2018 a cibiyar asibitin da ke Shika a Zariya.
A lokacin wannan aiki da za a yi, a cewar Farofesa Adamu Ahmed, ana sa ran kwararru kan fidar zuciya daga asibitin kula da cutar zuciya ta kasar Ghana za su kasance a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, domin aiwatar da fidar da za a yi wa wadanda ke fama da
wannan cuta ta cutar zuciya. Da kuma mataimakin shugaban asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Farofesa Adamu Ahmed ke amsa tambayoyin wakilinmu kan yadda asibitin ke gudanar da ayyuka a tsakaninsu da ma su lalurai daban –daban da suke zuwa asibitin, Ya ce, a duk rana suna samun karin ma su zuwa asibitin a dalilin matsalolin rashin lafiya da ke addabarsu.
Zuwa yanzu kuma, kamar yadda Farofesa Ahmed ya ce, mahukumtan asibitin suna samun marasa lafiya daga kasashen Jamhuriyyar Nijar da Kamaru da Chadi da kuma kasar Ghana da wasu kasashen Afirika. A karshen ganawar da wakilinmu ya yi da ,mataimakin daraktan asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Farofesa Adamu Ahmed, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyi ma su zaman kansu da suke ciki da wajen Nijeriya da kuma ma su tallafa wa al’umma, da su tallafa wa asibitin da kudade, domin samar da yanayin da asibitin zai sami damar
fuskantar ayyukan da aka dora ma sa, na kudaden da za su warware ko wane irin matsalolin kiwon lafiya da ke addabar al’ummar da suke zuwa asibitin daga ciki da kuma wajen Nijeriya.

Advertisement
Click to comment

labarai