An Shawarci Masu Zaben Fidda Da Gwani Na Jam’iyyar APC Daga Fagge — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Shawarci Masu Zaben Fidda Da Gwani Na Jam’iyyar APC Daga Fagge

Published

on


Anyi kira ga masu ruwa da tsaki a zaben fidda Gwani na cikin jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Fagge akan su zabi dan takara majalisar jaha dazai amfanarda al’umma da akeda tabbaci da kyakkyawan tunanin idan an sashi a gaba zai fidda jaki daga duma jama’a kuma su yaba. Me neman jam’iyyar APC ta tsai dashi takarar neman majalisar jaha a karamar hukumar Fagge.Alhaji Umar Usman Sule da a kafi kira da Shakara ya yi wannan kiran.
Yace suma wakilai masu zabe in sukayi kyakkawan zabe al’umma zasu ce sun kyauta musu. Da yawa yan siyasa in suka fito abubuwa daya suke maimaita wa nako zan yi kaza –zanyi kaza amma da sun hau sai aji shiru abin takaici.
Shakara ya yi nuni da cewa a bangaren kudancin kasar nan kafin a fidda mutum sai an duba anga mai ya yi wa wace gudummuwa yake bayarwa sannan inya cancanta a zabe shi.Wakilai masu zabe suyi duba an zabi wasu a baya kuma wace gudummuwa suka bai wa jama’a in suka yi awo suka duba ya kamata su dauki mutumin da ke bada gudummuwa.
Ya ce, ba sai mutum yana da kudi ba zai bada gudummuwa ba, in malamin makaranta ne ko bai da kudi da iliminsa zai taimaka ta bada ilimi, kyakkyawar mu’amala da abubuwa na bada gudummuwa da dama da ake a cikin al’umma sais u duba suga irin rawarda mutum ya taka da cancanta a kawarda maganar kudi a zabi duk wanda akaga cewa yanada mu’amala wanda in aka sashi a gaba zai taimaki cigaban al’umma a zabe shi.
Alhaji Umar Shakara ya bayyana cewa a ka’ida aikin dan majalisa shine yin doka dakai kuduri ba kamar yanda ake yanzu ba. Duk abinda ya taso yakamata a tuntubi al’umma daga mazaba kafin a zaratarda wani abu daya shafi al’umma .Bai kamata dan majalisa inya karbi aikin mazabu ya aiwatarda tunaninsa ba ka’ida shi ne yazo kowace mazaba ya nemi al’umma yaji me suke bukata, a wani wajen matsalar magudanan ruwa ke damunsu ,dan majalisa kuma ya dauki masallaci ya kawo, yakamata dan majalisa yasan duk abinda zaiyi shine bukatar al’ummarsa.
Shakara ya ce wannan takara da yake ta al’ummace, a baya ma ya taba takarar kansila a CPC a mazabar Fagge “D”.Wanda daga baya bayan anyi hadaka an kafa APC ya janyewa wani dan takarar da aka baiwa takara suka kuma dafa masa har yakai ga nasara.Tun daga nan yake cikin harkokin siyasa da bada gudummuwarsa.
Yace bama a dalilin siyasa ba, dama ya taso yanada kishin ganin ya tallafawa cigaban al’umma ta fannin lallafawa harkar lafiya da ilimi da samarda aiki ga al’umma tun samada shekaru 15.Cikin irin gudummuwa da yake bayarwa a fannin lafiya sun hada da sayawa marasa lafiya magumguna da ake rubuto musu a Asibitoci in basuda hali suna kawowa a saya musu tare da tallafawa marayu da kayan makaranta da littattafai da tallafawa wadanda suke ma a manyan makarantu da kudin rijista da sauran tallafi daidai gwargwado.
Ya kara da cewa, ana kuma daukar matasa aikin yi musamman a bangaren harkarsa ta tela da kuma harkar kasuwanci da yake wanda a yanzu haka akwai matasa da suka kusa 40 da ya samawa damar aiki a karkashinsa da kai wasunsu a wasu wurare.
Ya ce, samar da aiki ga matasa wata kafa ce da zata kauda zaman banza da hana shaye-shaye a cikin al’umma da kowa ya kamata yasa hannu dan kauda wannan matsala, ya ce, irin haka Jagoransu a siyasar Fagge Dan majalisar tarayya mai wakiltar Fagge Kwamred Aminu Sulaiman Goro yake wajen samawa mutane aiki wanda yanzu haka samada mutane 700 sun sami aiki a fannoni da dama.
Dan haka suke kokarin suyi koyi dashi in Allah ya basu dama wajen ganin sun dafa wa irin kokarin da yake a wannan takara ta majalisar jiha da yake neman takara.
Alhaji Shakara yace tun farko wannan takara mutanene suka fito dashi bama da saninsa ba ta kafafen sada zumunta aka rika aikawa cewa ya fito takara kuma aka bugo masa waya ana tambayarsa gameda takarar dabai san zaiyi ba,amma daya bincika sai ya samu wasu mutanene suka amince ya fito ba tareda sun tuntubeshi ba,daya nemi jin dalilinda yasa basu tuntubeshi ba kafin tsaida matsaya, sun nuna masa cewa saboda ma karya zo musu da wani abu na daban shi yasa suka sanar kuma hakan bukatar al’umma ce.
Yace a haka yayi tuntuba tsakanin abokai da iyaye da jagorori sannan ya amsa yrake kan neman takarar wanda babban ginshikin abinda ya dora takararsa akai shine cigaba da dorawa akan abinda ake na tallafawa cigaban harkar lafiya,ilimi da samarda ayyukanyi da zai dora dan bunkasawa inya sami zama dan majaliosar jihar Kano dan wakiltar Karamar Hukumar Fagge.
Umar Usman Shakara Yayi nuni da cewa cikin burinsa akwai gyara Asibitin Sabo Garba dake unguwar Fagge wanda a yanzu ke cikin wani hali na kunci duk da irin taimakawa da Asibitin keyi wajen kulada lafiya amma yana kuntataccen idan anyi ruwa wajen kan jagwale duk da cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar Fagge yay kokari yasai wani gida dan fadada asibitin amma saboda hurumin Gwamnatin jahane sai hakan bai samu ba dan haka idan yakai ga nasara zaiyi kokari yaga an maida Asibitin babba ta mai dashi mai hawa Biyar dasa masa kayan aiki na zamani da karinma’aikata da samarda wasu Asibitocin a sassa daban-daban dan anfanin al’umma.

Advertisement
Click to comment

labarai