Rikici Tsakanin NNPC Da Kanfanonin Mai Na Kawo Cikas Ga Zuba Jari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Rikici Tsakanin NNPC Da Kanfanonin Mai Na Kawo Cikas Ga Zuba Jari

Published

on


‘Yan maganganun na rashin fahimtar juna da suke faruwa tsakanin hukumar kula da albarkatun mai ta kasa, da kamfanonin man kasa da kasa dangane da yadda za a rika rarraba kwangiloli al’amarin yana kawo matsala akan ci gaba da sanya hannun jari. Saboda matsalolin da ake fuskanta wajen samar da kudade, abin ya yi sanadiyar koma bayan hadin gwiwa a banagaren mai da kuma iskar gas.

A karkashin PSHs da kuma NNPC sun tattauna da kuma samom matsaya,  sai dai kuma su ‘yan kwangilar( yawancinsu IOCs) akan kudaden ci gaban harkar  hako mai daga rijiyoyin karkashin ruwa, domin a samu damar cika gibin, bayan  an samu wasu kudade da suke na haraji.

Da yake tana fama da yadda kudaden shiga  ta bangaren mai suka ja baya, Nijeriya ta bada sanarwa a shekarar 2015 ta shirya sake duba al’amarin kudaden haraji na bangaren man fetur, da kamfanonin kasashen waje, har ta dauki mataki na karin su kudaden da ake biya a wurin da ya wuce mita 1,000 daga zeo zuwa kashi uku, na man da aka hada wanda ya kai bare 50,000 ko wacce rana.

Ana dai ci gaba da yin taron fahimtar juna tsakanin NNPC da kuma’yan kwangilar PSC akan dukkannin wasu koke koke. Babbar manufar ita ce don a tabbatar da ci gaba da sa hannun jari, wadanda IOCs, suke yi, da kuma yadda za a ci gaba da yin kakaka. Ga kuma yadda za a samu damar tsayawa akan kashi 47 na na jarin da ake da shi. Shugaban hukumar kula da albarkatun mai ta kasa, Dokta Maikanti Baru ya bayyana lokacin da yake gabatar da takardar shi, a wani taro wanda aka yi a Legas makon daya wuce.

A karkashin  tsarin JB duk NNPC da kuma  kudaden IOCs n a ci gaban wurin aiki, kudaden aiki, ta hanyar wasu kudaden da ake kira su da inda aka ajiye su, daga nan kuma za a samu wani kaso na danyen man, da aka samu wanda kuma na gwada shi ne, da yadda kason  shi JBC  a hannun jarin.

Shi ma da yake gabatar da jawabin sa lokacin taron shugaban Bankin Stanbic IBTC Mr Demola Sogunle, ya bayyana cewar a taron kasa da kasa na shekara shekara, na nuna kayayyaki na kungiyar  injiniyoyin bangaren man fetur. Ya kuma bayyana cewar shi JP ya hadu da matsaloli a shekarun da suka wuce, babban al’amarin kuma shi ne  a kan kudaden ayyukan samar da mai da kuma iskar gas.

‘’Harkokin hakar main a JB abin ya smu koma baya tun shekarar 2010, wannan kuma ya kasance haka ne saboda, an samu kma baya ta bangaren sa hannun jari a kaddarorin JB wanda IOCs ya  zama sanadiyya.

A watan Disamba 2016 hukumar kula da albarkatun  mai ta kasa, ta bar tsarin yadda ake kawo wasu kudade daga Bankuna, ta duba wata hanya da za a rika samun taimako.

Kamar dai yadda Sogunle ya bayyana matakin da gwamnati ya dace ta dauka, domin taimakawa yadda kamfanin JB sai samu ya sake tsayawa da kafafun shi biyu, abin ya hada da sabunta lasisi, amincewa da dokar bangaren man fetur ( abinda ya shafe kudade zalla ) lura da harkar tsaro , sai kuma matsalolin da suka damu al’umma, ga kuma maganar lura sosai da kuma karewa da duk kayayyakin da za a fitar zuwa kasashen waje, har zuwa wurin da za a sauke su.

Shugaban hukumar kula da albarkatun mai ta kasa har ila yau ya kara, dangane da abubuwan da suka taimaka wajen koma bayan yadda JB  a shekaru goma wadanda suka wuce.

Ya ci gaba da bayanin cewar ‘’ Ita masana’antar tana bukatar ta yi kamar da gaske take, wajen neman duk hanyar data dace, bude dujk wata kafa da ake ganin hakan ya taimaka wajen koma bayan yadda shi kamfanin yake yin aikin shi shekarun baya. Akwai ma maganar yadda al’umma suke kashe kudade, wato yadda abinn ya ragu, ga kuma maganar yadda ba a samun masu sa hannun jari, wanda hakan ma ya taimaka shiga halin da ake ciki.

‘’Domin a samu cimma manufa saboda ci daban bangaren manfetur, abinda aka sann yana taimaka ma Nijeriya, yana da kyau matuka da dukkan wadanda suke da ruwa da kuma tsaki a bangarn mai su hada kansu domin shawo kan matsalolin da suke damuwar bangaren man fetur.   Ga kuma yadda ake taimakawa JB da kudade sai kuma ariyas na kudaden da ba a biya ba, da kuma taron cimma matsaya da ake yi domin fita daga matsalolin PSC.’’

Baru ya kara bayyana cewar ita aka samu shawo kan matsalar samar da kudade ga JB, hakan zai sa a samu karuwar man da ke tonowa , wanda ake sa ran zai fi barel milyan 1 da dubu dari biyu ko wacce rana, nan da shekarar ta 2025, ta hakan sai masu sa jari da kuma gwamnati duk hankalinsu ya kwanta.

 

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai