’Yan Bindiga Sun Kashe Mai Taimaka Wa Tsohon Gwamna A Ekiti — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Mai Taimaka Wa Tsohon Gwamna A Ekiti

Published

on


Akalla mutane uku ciki har da mai tallafa wa tsohon gwamna Segun Oni; Mista Bunmi Ojo ne suka bakunci lahira a daren ranar Juma’ar da ta gabata yayin wnai hari wanda wasu ‘yan bindiga suka kai a Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti.
Kafin mutuwarsa, Bunmi Ojo shi ne Kwamishinan hukumar ‘Federal Character Commission’, an harbe shi ne a sakamakon wani harin ba-zata da wasu ‘yan bindiga suka kai damisalin karfe 10:00 na dare a lokacin da suke kallon kwallon kafa a wata cibiyar kallo da ke yankin Adebayo, inda mummunan lamarin ya rutsa da wasu abokansa su biyu.
Sai dai har zuwa yanzu ba a iya ga gano wadanda suka kai wannan farmakin ba. wata majiya ta shaida wa ‘yan jarida cewa,, ‘yan bindigan su Shida sun kewaye wajen kallon kwallon kafar inda nan take suka harbe Ojo.
Ojo wanda yana daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar APC, an harbe sa ne a tsakar kansa da kuma cikinsa, inda aka kuma kai gawarsa zuwa asibitin koyarwa da ke Ado Ekiti.
Wata majiya kuma ta daban, ta shaida cewar marigayin yana da muradin tsayawa takara a zaben 2019 da ke tafe, inda ke da muradin neman kujerar dan majalisar wakilai ta tarayya da ke wakiltar mazabar Ekiti ta Arewa wanda ya hada da Ido/Osi, Ilejemeje da Moba.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Da yiwuwar wannan harin ya zama shiryayye daga abokan hamayyarsa ta siyasa, kasantuwar ya fara samun gungun jama’a suna mara masa baya kan wannan muradin nasa,”
A wata majiyar kuwa, an ce ‘yan mafiyan da suke yankin ne suka aikata aika-aikar, “Mutane da dama an kashe su a yanki Adebayo kwana-kwanan nan. gaskiya, mu mun iya fahimtar kawai ‘yan kungiyar asiri ne suka kashe-kashen nan, domin suna ganin wuraren kallon kwallon suna taka musu birki wajen gudanar da harkokinsu domin haka ne suke son a daina fitowa kallon cikin dare domin su samu su ci gaba da aiyukansu, ina tunanin haka ne ya faru da shi Ojo.
“Wannan harin, wanda har ya shafi Bunmi Ojo ina ganin ba shi zalla suka nufa ba, kai dai za a iya cewa sun yi harbin kan mai uwa da wabi ne,” Kamar yadda majiyar ta shaida
Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti DSP Caleb Ikechukwu hakan ya ci tura.
Sai dai, tunin gwamnatin jihar Ekiti ta yi Allah wadai da wannan harin, a wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya wanda ke dauke da sanya hannun babban mai tallafa wa gwamnan jihar kan harkokin sadarwa da kafafen zamani, Lere Olayinka, gwamnatin ta kuma mika sakon jajenta ga iyalai, ‘yan uwa da abokan wadanda aka kashe, hadi da addu’ar Allah albarkaci matansa da iyalansa da ya bari.
Har-ila-yau, Gwamnan jihar Kayode Fayemi ya nuna alheninsa da jimaminsa kan harin, inda ya bukaci jami’an tsaro su tashi tsaye domin zakulo wadanda suka kai harin don a hukunta su.

Advertisement
Click to comment

labarai