Connect with us

WASIKU

‘Makirci Ya Sa Aka Raba Tsakanin Buhari Da Kwankwaso’

Published

on


Salam, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, don Allah ku bani dama in fadi irin nawa ra’ayin a kan makircin da aka yi wajen raba shugaban kasa da kuma Kwankwaso.
In sha Allahu babu kokwanto a kan Buhari zai zarce, ni dai ko girgiza bana yi a kan zarcewan shugaba Buhari, muna kaunar Buhari ba don wata tarkacen jam’iyyar APC ba. Shi dai shugaba Buhari ya fi karfin a zabe shi don wata jam’iyyar hayaniya APC da ta tarkato azzalumai, barayi da kuna maciya amana a cikinta, kyawawan dabi’arsa ita ce jam’iyyarsa wanda duk duniya an shaide shi a kan haka.
Don haka babu kokwanto zai zarce, an zabe shi ya zama shugaban kasa a lokacin da bashi da sojoji, kuma bashi da ‘yan sanda da za su kare masa miliyoyin kuri’ar da talakawa suka bashi, yanzu duk yana da su kuma suna cikin karkashin umarni da ikonsa suke.
To amma abin da duk wani mai hankali zai duba shi ne, shugabanci ba na mutum daya ba ne, shugaba Buhari yana da bukatar samun nagartattun mutane tun daga matakin kansila har zuwa sanata domin su ta ya shi mulki a gyara kasa, a farfado da Arewa daga muguwar kisan da makiya suka yi mata.

Har ila yau, muna da kyakkyawan zato a kan Kwankwaso cewa dan kishin Arewa ne. Abin lura daga cikin kyakkyawan zato da ake masa ne ya sa shugaba Buhari ya gayyace shi tattaunawa da tsakar dare, a wanni kadan bayan tattaunawar kafin ya fice daga APC, muna iya fahimtar cewa shugaba Buhari ya fi kowa sanin muhimmancin Kwankwaso shi ya sa ya yi masa kara da mutuntaka har ya gayyaceshi tattaunawar sirri tsakar dare. Gayyatar da Buhari ya masa kalubale ne ga mutanen da suke ganin kamar Kwankwaso ba wani abu bane.

Kunga tunda siyasa ake yi a tsarin mulki karkashin jam’iyya duk wani muradin shugaba Buhari to yanzu Kwankwaso da mutanensa ba za su goyi baya ba tun da sun fice daga APC, ba za su hada kai tsakanin PDP da APC a gyara Nijeriya ba, sai dai ma su yi fatan ganin Buhari ya gaza sai su dinga samun hanyar da za su soke shi su kuma tallata hajarsu.

Wallahi ina da tabbaci kuma har da shaidu da zan iya kare kaina a gaban kowaye, tabbas zuga Kwankwaso aka yi domin ya aikata wannan mummunan aiki, akwai dan majalisa da ya ce wallahi hatta cikakken bacci basa yi saboda su tabbatar ba a samu sulhu tsakanin Kwankwaso da Gwamna Ganduje ba, har bokaye suka gayyata domin kar a yi sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje. Wannan al’amari abun takaici ne ga mutanan Arewa kai harma da kasa baki daya.

Fatansu wadannan mutane masu hada makirci shi ne su nemi wata hanya da za su bi domin lalata mana manyan mutane daga yankinmu masu hazaka da kishi da gaskiya da rashin tsoro. Idan har ba su samu nasarar raba su da nunfashi ba, kamar yadda yanzu suka ci nasarar zubar mana da mutuncin Kwankwaso a idon miliyoyin masoya shugaba Buhari, za su bari sai lokacin da Buhari ya gushe Kwankwaso ya taso sai su juya masa baya, sun yi irin haka a wasu kasashen da suke da rikitaccen tsarin siyasa da gwamnati wanda akwai addinanci da kabilanci da bangaranci a cikinta irin wanda muke fama da shi a Nijeriya.

Duk cikin manyan ‘yan siyasar kasar nan wadanda suka fito daga yankin Arewa da suke hayani cewa za su mulki Nijeriya, babu wanda ya kai Kwankwaso cancanta bayan shugaba Buhari, amma yanzu an samu nasarar raba tsakanin Kwankwaso da Buhari. Mu ajiye wannan a cikin zuciyarmu sai sun juyawa Kwankwaso baya idan lokaci ya yi.

Mu yi addu’a Allah ya fahimtar da Kwankwaso domin ya fahimci masoyansa na asali ya kuma gane makiyansa na asali. Na so a ce tun farko Kwankwaso ya zama dan gani kashenin Baba Buhari mai gaskiya, domin ya samu shugabanci a shekarar 2023 idan Allah ya kai mu. Amma duk da haka bai makara ba, zai iya gyara kuskuren da ya tafka kuma kima da mutuncinsa ya dawo a idon masu hankali da tunanin makomar yankin Arewa.

Muna yiwa wadannan shugabannin fatan alheri, Allah ya shiga tsakaninsu da munafukai masu yin makirci a tsakaninsu.
Sako daga Muhammad Idris (Babanne), Abuja.
7065279510

Jinjina Ga Maryam Bagel
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.

Ina ya bawa tare da jinjina wa ‘yar majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Dass a jahar bauchi. Domin kuwa ta zama kallabi tsakanin rawuna! Ya kamata sauran takwarorinta su yi koyi da ita wajen jajircewa da kuma inganta rayuwar al’ummarta.
Sako daga Nasiru Albani, Bauchi. 081617155483

Wai Komi Sai An Siyasantar Da Shi Ne?
Salam, Editan LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ka bani dama na bayyana abin da ya ke ci min tuwo a kwarya. Abun dubawa wai a ce komi sai an saka siyasa a cikin sa.
A kwanakin baya ne ma’aikatar ayyuka da gidaje da wutar lantarki na tarayya ta sanya sunayen wasu garuruwa daga Kaduna zuwa Zariya wanda aka samu kura-kurai wajen rubutun.

‘Yan siyasa sun sami damar jefa albarkacin bakinsu wajen yada manufarsu na siyasa a yayin da wasu suke alakanta faruwar lamarin ga gwamnati da sakaci na gwamnati, ko da yake abun haushi babu wata kafa musamman na Arewa da ta yi tsokaci a kan abun. An bar wa ‘yansiyasa suna ta cin karensu babu babbaka wajen nuna cewa kokarinsu ne aka gyara.

Wani yaron Sanata Shehu Sani ya nuna cewa an yi wannan gyara sakamakon kokarin mai gidansa sanata, amma kuma wani mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna ya soki wannan ikararin na yaron Sanatan ya nuna cewa ai Gwamnatin jihar Kaduna ce ta tsaya kai da fata ta gyara.

Mu dai a nan kiranmu ga al’umma shi ne su lura da abubuwan da ke zuwa yake dawowa wajen sanin abubuwan da zai kawo masu ci gaba da inganta su.

Kamata ya yi jama’a su yi korafin kamfanonin da ake bai wa kwangilolin iron wadannan ayyuka da dalilan da ya sa ake zuwa Kudu a dauko wadanda za su yi kwangilar rubuce-rubuce da Hausa bayan akwai kamfanoni bila adadin da za su yi wadannan ayyuka a Arewa.

Siyasa dai kar ta sanya mu makance mu rasa ina ne Gabas ko Yamma, mu kuma rasa gano hanyar ci gabanmu. Allah ya sa mua dace, amin.
Sako Daga Usman Hamisu,Kaduna.
08160874213


Advertisement
Click to comment

labarai