Connect with us

LABARAI

Zaben Jihar Ekiti: APC Ta Fadi Dalilin Tura ‘Yan Sanda Har 30,000

Published

on


Jam’iyyar APC ta ce, jami’an ‘yan sanda dubu Talatin da aka tura Jihar Ekiti, ya zama tilas ne domin tabbatar da an gudanar da zabengwamnan Jihar lami lafiya a yau din nan Asabar.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren ta na yada labarai, Bolaji Abdullahi, ya fitar a Abuja, ranarAlhamis.
Wannan kalaman na Jam’iyyar ta APC martani ne kan zargin da Jam’iyyar adawa ta PDP ta yinacewa an tudado ‘yan sandan ne domin a musgunawa magoya bayanta su zabi dan takarar Jam’iyyar ta APC, Dakta Kayode Fayemi, da karfintsiya.
“Ai kamar yadda aka saba ne a kowane zabe, akan kawo karinjami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya ta yadda za a gabatar da zabe mai inganci.
“Bisazargin da Jam’iyyar PDP ta yi a cikin sanarwarta, ga dukkan alamu shugabannin Jam’iyyarna kasa ba su san gaskiya na bin da ketafiya ba a Jihar ta Ekiti, kokuma in sun sani suna dai son karkatar da hankulan mutane ne dai kawai,” in ji APC.
Jam’iyyar ta APC ta kwatanta halayyar da Gwamna Ayodele Fayose, na Jihar ta Ekitiya nu na a ranar Laraba da was an kwaikwayo, ta ce, ai a sarari yake, yana dai son ya nu na wa duniya ne kamar wai ana tusguna masa.
“Fayose, ya mayar da batun takarar nan tamkar da shi ne ake fafatawa, alhalin kuwa sam ba haka ne ba; ai takarar ana yi ne a tsakanin DaktaFayemi da Farfesan da yaketa kokarin boyekansa a tsakankanin yatsun Fayose din.
“Abin da dukkanin masu zabe suka fahimta a Jihar Ekitishi ne, zaban Farfesan tamkar bai wa Fayose wani wa’adin mulkin ne na uku, to kasantuwan yadda suka sha wahala a karkashin mulkinsa ne ya sanya suka yi watsi da su duka biyun,” in ji APC.
A cewar Jam’iyyar ta APC, PDP ta rigaya ta san sakamakonta a Jihar ta Ekiti, ta san ta rigaya ta fadi a zaben, borin kunya kawai take yi da wadannan zarge-zargen.
Jam’iyyar ta ce har yanzun, mutane ba su manta da yadda Fayose ya yi amfani da Jami’an tsaro wajen murda zaben da ya gabata ba a Jihar ta Ekiti.
“Abin takaicin a gare shi shi ne, a wannan karon ba zai sami wannan daman ba, a ci zabe ba magudi wannan wani bakon al’amari ne shi a gare shi, shi ya sanya ya bi duk ya damu.
“Sam ba abu ne da yakamata ba, ga Jam’iyyar ta PDP ta ci gaba da irin wannan koke-koken na cewa wai ‘yan sanda sun ci mutuncin Fayose, a ranar Laraba, bayan da shi kansa Fayose din ya bai wa ‘yan sandan hakurin cewa ya yi wa jami’ansu karya.” In ji APC.
Ta tabbatar da cewa, shawarar karshena kowane ne zai zama gwamnan Ekiti yana hannun jama’ar Jihar ne, wanda kuma za su tabbatar da hakan a yau.


Advertisement
Click to comment

labarai